Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid za ta rage albashin daraktoci da koci da 'yan wasanta
Daraktoci da koci da 'yan wasan Real Madrid za su rage kaso 10 zuwa 20 na albashinsu, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da coronavirus ta jawo.
A cikin watan Maris aka dakatar da wasannin tamaula a Spaniya, bayan da kasar ta ayyana dokar ta baci saboda annobar.
Real ta ce 'yan wasa da koci da ma'aikatanta ne suka cimma shawarar rage albashin don kauce wa sallamar wasu a aiki.
Haka ma kungiyar 'yan wasan kwallon kwandon Real Madrid sun amince don radin kansu a rage musu albashin saboda halin matsi da aka shiga.
A watan jiya ne aka sanar 'yan wasan Barcelona sun amince a zabtare musu kaso 70 cikin 100 na albashinsu don kar wasu ma'aikatan su rasa aikinsu.
Haka kuma 'yan kwallon sun cimma yarjejeniya cewar za su yi gudunmuwa don tallafawa kananan ma'aikata.