'Yan Barcelona sun rage albashi saboda coronavirus

'Yan wasan Barcelona sun amince a zabtare musu kaso 70 cikin 100 na albashinsu, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki saboda coronavirus.

Wannan yunkurin zai taimaka wa kungiyar ta biya dukkan albashin ma'aikatan da suke mata aiki.

Kyaftin Lionel Messi ya ce sun jinkirta da wannan shawarar, bayan da 'yan wasan ke neman hanyoyin da ya kamata su taimakawa kungiyar.

A karshen mako, kocin Juventus, Maurizio Sarri da 'yan wasa suka amince da yafe albashin wata hudu.

Mutum 7,340 ne suka mutu a Spaniya saboda coronavirus, kasa ta biyu a duniya da ta fi kamuwa da annobar, bayan Italiya.

'Yan kwallon kungiyar Bayern Munich da Borussia Dortmund duk sun amince a rage musu albashi.

Haka ma daraktocin Barcelona da 'yan wasan kwallon kwandon kungiyar duk sun amince za su rage albashinsu.