Wasu kungiyoyin Jamus sun yi atisaye ranar Litinin

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich tana daga cikin kungiyoyin da ke buga gasar Bundesliga da ta koma yin atisaye ranar Litinin.
Wannan ne karon farko da kungiyoyin suka koma fili tun bayan bullar coronavirus.
Banda Bayern Munich, ita ma Borussia Monchengladbach da kuma Wolfsburg duk sun yi atisaye a karon farko ranar ta Litinin.
Munich ta yi atisayenta da 'yan wasa biyar a wari daya, amma ba sa hada jiki, inda suka bai wa juna tazara.

Asalin hoton, Getty Images
Ita ma Paderborn wadda ke karshen teburi a Bundesliga ta gudanar da atisayen da 'yan kwallo ba suyi cudanya da juna ba.
Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Bundesliga ta Jamus, wadda ake sa ran ci gaba da ita ranar 30 ga watan Afirilu.
Mako biyu da suka wuce 'yan wasan Bayern Munich suka rage albashinsu, domin kungiyar ta fuskanci kalubalen tabarbarewar tattalin arziki saboda coronavirus.
Bayern ce ke kan gaba a kan teburin Bundesliga kan a dakatar da wasanni da tazarar maki hudu tsakaninta da Borussia Dortmund.

Asalin hoton, Getty Images










