Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus ta kashe tsohon shugaban Marseille
Coronavirus ta kashe tsohon shugaban Marseille, Pepe Diouf kamar yadda kungiyar ta sanar.
Diouf dan kasar Senegal ya shugabanci kungiyar daga 2005 zuwa 2009, inda Marseille ta yi ta biyu sau biyu a gasar Lique 1.
A zamaninsa Marseille kai wasan karshe karo biyu a kofin kalubalen Faransa da ake kch Cup.
A shekarar 2010 Merseille ta lashe French League a karon farko, bayan shekara 18.
Tsohon dan wasan tawagar Faransa da Liverpool, Djibril Cisse ya buga wa Marseille tamaula a lokacin da Diouf ke shugabanci.
''Kwallon kafa ya yi hasarar babban jami'i, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter ya kara da cewar ''Rana ce ta bakin ciki da rashin Diouf''.