An dage gasar Zakarun Turai saboda coronavirus

Watakila a buga wasan kwaf daya a Champions League da Europa League, bayan da hukumar kwallon Turai ta dage dukkan wasannin.

Bayan da aka dakatar da wasannin na kwallon kafa a kasashen Turai, saboda coronavirus, babu tabbaci idan za a karkare kakar wasannin bana kamar yadda aka tsara rufewa a karshen watan Mayu.

Ana kuma fatan karkare Champions League da Europa League cikin watan Yuni, inda ake sa ran buga gasa tsakanin kungiyoyin da suka rage a Istanbul da Gdansk domin fitar da zakara.

An kuma dage gasar mata ta Champions League da aka tsara buga wasan karshe ranar 24 ga watan Mayu.

Wani batun da ke da sarkakiya shi ne gasar Champions League ta maza, wadda aka buga wasa hudu na zagaye na biyu, yayin da aka buga wasan farko a hudu da ake sa ran buga zagaye na biyu.

A gasar Europa kuwa an buga wasa shida a zagayen farko, yayin da guda biyu suke kwantai.

Abu ne mai wahala Uefa ta kasa karasa wasan da aka buga zangon farko, amma za ta iya hakura da wanda ba a hadu a wasan farko ba - shi ne kungiyoyin Spaniya da za su kara da na Italiya.

Hukumar kwallon kafar Turan na fatan hada karawa daya tsakaninsu domin fitar da gwani, sannan a jefa kwandala wajen zaben filin da za a fafata.

Shi ma wasan daf da na kusa da na karshe da fafatawar daf da karshe za a yi su kwaf daya.