Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da dukkan wasannin tamaula a Spaniya
An dakatar da dukkan wasannin tamaula nan take a Spaniya har da La Liga, bayan da kasar ke yaki da coronavirus.
Tun farko an tsayar da gasar La Liga wasannin mako biyu a farkon watan Maris kafin kasar ta fara yakar annobar da ta sa dokar ta baci.
Kawo yanzu ba a san ranar da za a koma buga wasannin kwallo a Spaniya ba, har sai mahukunta sun tabbatar an dakile coronavirus.
Barcelona wadda ke rike da kofi ce ke kan gaba a gasar ta La Liga ta bana da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.
Tun farko mahukuntan La Liga sun dauki matakin dakile yada cutar, bayan da dan wasan kwallon kwandon Real Madrid wanda ya yi atisaye da kayan da masu buga kwallo ke yi aka aka sameshi da coronavirus.
A ranar Lahadi gwamnatin Spaniya ta tsawaita dokar ta baci da ta saka a farkon Maris yanzu ya koma 11 ga watan Afirilu.
Wadanda aka samu sun kamu da cutar ranar Litinin ya karu zuwa 33,089 daga 28,572 da aka samu a baya.
Kimanin mutane 2,182 ne suka mutu a Spaniya, sakamakon coronavirus.