Naismith ya amince a rage albashinsa saboda coranavirus

Kyaftin din Hearts, Steven Naismith ya amince a zabtare masa kaso 50 cikin dari na albashinsa domin kungiyar ta ci gaba da rayuwa.

Hearts mai buga gasar Premier ta Scotland ta umarci 'yan wasa da jami'ai da ma'aika su amince su rage albashinsu, saboda halin tabarbarewar tattalin arziki sakamakon coronavirus.

Mai kungiyar Ann Budge, ya ce Hearts za ta yi hasarar kudin shiga da zai kai fam miliyan daya, sakamakon dakatar da wasannin kwallon kafa da aka yi.

Naismithh, mai shekara 33 ya ce zai bayar da goyon baya ga abokan taka ledarsa bisa hukuncin da kowanne zai amince da shi.

Kungiyar ta ce matakin da ta dauka zai hana a sallami wasu daga aiki sakamakon matsin tattalin da aka shiga bisa annobar da ta addabi duniya.