Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fellaini ya kamu da Coronavirus
Tsohon dan kwallon Manchester United, Marouane Fellaini ya kamu da cutar coronavirus.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan wasan mai shekaru 32 wanda ke murza leda a kungiyar Shandong Luneng na China, ya ce yana saran ya koma buga kwallo da zarar ya warke.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na China sun ce Fellaini yana can a kadaice a wani asibiti mai suna Jinan.
Dan kwallon Belgium din ya koma China ne a shekara ta 2019, bayan shafe shekaru 11 a gasar Firemiya ta Ingila tare da United da Everton.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce "Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa dan wasansu Fellaini ya kamu da cutar."