Coronavirus ta kashe tsohon shugaban Real Madrid

Tsohon shugaban kungiyar Real Madrid, Lorenzo Sanz ya mutu a ranar Asabar bayan da ya kamu da cutar coronavirus.

Sanz mai shekaru 76, shi ne shugaban Real tun daga shekarar 1995 zuwa 2000, a lokacin da kungiyar ta lashe gasar zakarun Turai har sau biyu.

"Mahaifina ya rasu," in ji dan Sanzs wanda ya rubuta haka a shafinsa na Twitter.

Sanz ne ya siyo manyan 'yan wasa irinsu Roberto Carlos, Clarence Seedorf da kuma Davor Suker a lokacin da yake jan ragama a Bernebeu.

Ya fadi zaben shugabancin kungiyar a takara tsakaninsa da Florentino Perez a shekara ta 2000.