Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa faruwa a duniyar tamaula
Tuni Real Madrid ta fara shirye-shiryen tarbar lokacin bazara kuma za ta iya bai wa dan wasanta na gaba Gareth Bale mai shekara 30 damar tafiya wata kungiyar a matsayin dan wasan aro. (Marca)
Manchester City ta sanya farashin fam miliyan 80 ga dan wasan gaba dan Aljeriya Riyad Mahrez mai shekara 29, wanda ake alakanta shi da koma wa Paris St-Germain. (Sun)
Manchester United na shirye-shiryen yin wani kokari na daukar dan wasan Barcelona da Faransa mai shekara 26 Samuel Umtiti, a wannan bazarar. (Talksport)
Dan wasan Atletico Madrid da Ingila Kieran Trippier mai shekara 29, ya bayyana cewa yana son yana son ya yi ritayarsa ne a tsohuwar kungiyarsa ta Burnley, kuma zai koma Gasar Premier ya yi wasa a Turf Moor karkashin Sean Dyche. (Sky Sports)
West Ham ta ce za ta samu damar karashe wasanta da za ta yi a gida a filin wasan da ke Landan, idan aka ci gaba da kakar wasan nan har cikin bazara, duk da kuwa cewa akwai wasu wasannin kamar baseball, da wasan tsere da kuma bikin casu. (Standard)
Kocin Arsenal Mikel Arteta yana son ya sayar da dan wasan tsakiya dan Armenia, Henrikh Mkhitaryan mai shekara 31, a lokacin bazara, kuma Roma ta kagu ta mayar da shi dan wasnata na dindindin daga yarjejeniyar aronsa da ta yi. (Express)
Rahotanni sun ce arzikin mamallakin kungiyar Chelsea dan kasar Rasha Roman Abramovich mai shekara 53, ya ragu da fam biliyan 2.4 a bana saboda annobar coronavirus, duk da cewa har yanzu yana da fiye da fam biliyan 10. (Star)
Dan wasa Jetro Willems mai shekara 25, da yake zaune aro a Newcastle daga Eintracht Frankfurt, ba zai sake wani wasa ba a 2020 saboda raunin da ya ji a gwiwars ya wuce yadda ake tsammani. (Bild, via Newcastle Chronicle)