La Liga: 'Yan wasan Valencia 5 sun kamu da Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Valencia da ke buga gasar La Liga a Spaniya guda biyar sun kamu da cutar Coronavirus.
Kulob din ya ce 'yan wasan suna ci gaba da murmurewa yayin da ake ba su kulawar da ta dace.
Dan wasan bayan kungiyar kuma dan kasar Argentina, Ezequiel Garay ne dan wasa na farko a La Liga da ya bayar da sanarwar kamuwa da cutar a ranar Lahadi.

Asalin hoton, Getty Images
Tun a ranar Alhamis ne aka dakatar da gasar ta La Liga bayan an killace tawagar Real Madrid.
Kasar Spaniya ce kasa ta biyu da cutar ta fi kamari a Nahiyar Turai bayan Italiya kuma tana kokarin saka dokar-ta-baci ranar Litinin.
"A bayyane take ban shiga shekarar 2020 a sa'a ba," Garay mai shekara 33 ya wallafa a Instagram.
"Garau nake, wajibi ne na yi biyayya ga hukumomin lafiya kuma na killace kaina."
Wani bayani da Valencia ta fitar ya ce 'yan wasan da abin ya shafa "suna cikin gidajensu cikin koshin lafiya kuma a killace".
"Muna da tabbacin cewa cikin hadin kai da yin aiki tare za mu kawo karshen wannan annobar," in kulob din.
A bangaren Real Madrid, wani dan wasan kungiyar na kwallon kwando ne - wanda ya yi atasaye a filin da Madrid din suka yi - ya kamu da cutar, abin da ya jawo aka killace 'yan wasan.
'Yan wasa da dama sun kamu da cutar a Serie A ta Italiya, ciki har da dan wasan aro daga kungiyar Wolves mai suna Patrick Cutrone.











