An killace 'yan wasan Real Madrid saboda coronavirus

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bai wa dukkan 'yan wasanta umarnin killace kansu bayan da wani dan wasan kwallon kwando na kungiyar ya kamu da cutar coronavirus.

Kazalika an dage duka wasannin Gasar La Liga na tsawon mako biyu.

'Yan kwallon kafa da 'yan kwallon kwando na kungiyar na amfani da bandaki guda, abin da ya jawo daukar wannan mataki.

Jami'an La Liga sun gana da Hukumar Kwallon Kafa ta Spaniya (RFEF) da Kungiyar Kwallon Kafa ta Spaniyar ranar Laraba da Alhamis kafin su yanke wannan hukuncin.

Dama dai tawagar kwallon kafa ta Real Madrid din za ta fafata ne da Eibar a La Liga ranar Juma'a ba tare da 'yan kallo ba.

Spaniya na da sama da mutum 2,000 da suka kamu da cutar coronavirus.