Real na son sayen Kepa, Man City za ta sabunta kwangilar Kevin de Bruyne

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na duba yiwuwar dauko golan Chelsea Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, a bazara, a yayin da ake rade radin cewa Chelsea na sha'awar dan wasan Barcelona Marc-Andre ter Stegen da takwaransa na Manchester United Dean Henderson, mai shekara 22. (Star)
Kocin Manchester City Pep Guardiola na shirin sabunta kwangilar dan wasan Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 28, a kan £350,000 duk mako. (Express)
Golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 22, ya gaya wa abokan wasansa a Sheffield United cewa zai koma kungiyar a matsayin aro a bazara idan Manchester Unitedta ajiye shi a benchi.(Mail)
Dan wasan Jamus Emre Can, mai shekara 26, ya ce Manchester United ta yi masa tayin aiki-amma, kamar yadda tsohon dan wasan na Liverpool ya ce "nan da nan na yake shawara ba zan karba ba". A halin da ake ciki Can yana Borussia Dortmund a matsayin aro dagaJuventus. (Kicker - in German)
Arsenal ka iya zawarcin tsohon dan wasansu Donyell Malen, mai shekara 21 dan kasar Netherlands wanda ya koma PSV a 2017. (Le10Sport)
Vitesse Arnhemna son arondan wasanChelsea dan kasar Ingila Conor Gallagher, mai shekara 20, wanda Swansea ta karbi aronsa. (Sun)
Manchester United na da kwarin gwiwar cewa za su iya rarrashin Tahith Chong, mai shekara 20, ya ci gaba da zama a kungiyar, duk da yakeBarcelona, Inter da kuma Juventussuna son daukarsa.(Sun)
Tottenham na sha'awar sayo dan wasan baya a bazara kuma sun sanya ido kan dan wasan Croatia mai shekara 27 Borna Barisic, wanda farashinsa ya kai £22m kuma a halin yanzu yake zaman aro a Rangers. (90 Min)
Kocin Manchester UnitedOle Gunnar Solskjaer ya ce kungiyar na bukatar dauko 'yan wasa "biyu ko uku" kafin a yi mata kallo a matsayin wacce ke son daukar kofin Firimiya duk da kwazon da suka nuna kan Manchester City a karon farko cikin shekara 10. (ESPN)
Dan wasan Chelseadan kasar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, ya bayyana cewa an "hana" shi komawa Tottenham lokacin musayar 'yan wasa a watan Janairu. (90 Min)
Giroud ya ce ya yi sha'awar komawaInter lokacin musayar 'yan wasa a Janairu. (Calciomercato)
Dan wasanArsenaldan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, wanda ake rade radin zai bar kungiyar, ya jaddada cewa yana "cikin farin ciki" a kungiyar. (Mirror)
Chelsea na kan gaba wurin zawarcin dan wasan Aldershot mai shekara 17 Reece Wylie. (Team Talk)
Dan wasan Juventus da Argentina Paulo Dybala, mai shekara 26, ya shaida wa wakilinsa ya soke shirinsa na komawa Manchester United - lokacin da wakilin nasa ya zauna a ofishin Ed Woodward. (Calciomercato, via Mirror)
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce kashin da suka sha a hannun Real Betisda ci 2-1 shi ne wasa mafi muni da suka buga a kakar wasan bana. (Marca)










