Pele na Brazil na dari-darin barin gidansa

Pele

Asalin hoton, AFP

Gwarzon dan kwallon kafar Brazil, Pele, na dari-darin barin gida, saboda ba ya iya tafiya ba tare da an taimaka masa ba, in ji dansa.

A bara ne aka kai Pele, zakaran kofin duniya karo uku wanda ake cewa babu kamarsa a fagen tamaula a duniya, asibiti.

Pele, mai shekara 79, yana fama da ciwon kugu wanda ke bukatar abin da zai dinga taimaka masa, bayan da ake yawo da shi a keken guragu idan zai shiga mutane.

Pele ya ci kwallo 1,281 a wasa 1,363 da ya yi kaka 21 yana taka leda, har da 77 da ya ci wa tawagar Brazil a wasa 91 da ya buga mata.

Pele na fama da rashin lafiya a shekarun baya, har da aiki da likitoci suka yi masa a 2015 kuma karo biyu ya sake komawa asibiti tsakanin wata shida.

Edinho ya ce Pele sarki ne a fannin kwallon kafa, amma ka kalli halin da yake ciki, baya iya tafiya, baya samun sukuni kamar yadda yake so.