Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern ta ci gaba da jan ragamar teburin Bundesliga
Bayern Munich ta ci gaba jan ragamar teburin Bundesliga da maki daya, bayan da ta tashi 0-0 da RB Leipzig ranar Lahadi.
Bayern ta yi wasa shida a jere tana nasara kuma dalilin da ya sa ta hau kan teburin a makon jiya, bayan da Leipzig ta yi canjaras da Borussia Monchengladbach.
Leipzig wadda ta jiyarci Munich a wasan mako na 21 ta kasa zura kwallo a ragar da Manuel Neuer ya tsare kam.
Ita kanta Munich ta kai hare-hare ta hannun Thiago da kuma Leon Goretzka domin neman maki uku, amma hakan bai yi wu ba.
Timo Werner ya samu damar da ya kamata ya ci wa RB Leipzig kwallo, amma da ya buga sai tamaula ta baude ta kuma yi fadi.
Werner shi ne ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Bundesligar Jamus, bayan da yake da 20 a raga kawo yanzu.
Bayern ta bai wa wadda take ta uku a teburi Borussia Dortmund tazarar maki hudu, bayan da ta sha kashi a hannun Bayer Leverkusen ranar Asabar.