Ighalo ba zai yi atasaye da United ba saboda Coronavirus

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ighalo ya koma Man United a watan Janairu daga Shanghai Shenhua ta China

Dan wasan gaban Manchester United, Odion Ighalo, ba zai yi atasaye da kungiyar ba a kasar Sifaniya saboda ana tsoron za a iya hana shi komawa Birtaniya saboda annobar cutar coronavirus.

Birtaniya da sauran kasashe sun kara tsaurara tsaro a filayen jiragen samansu a yunkurinsu na dakile yaduwar cutar zuwa kasashensu, wadda ta samo asali daga China.

Dan Najeriyar mai shekara 30 ya je Manchester ne daga China bayan kungiyar ta dauke shi a matsayin aro a watan Janairu daga kungiyar Shanghai Shenhua.

"Zai so a ce ya bi tawagar domin ya kara sanin 'yan wasan sosai," kociya Ole Gunnar Solskjaer ya fada wa MUTV.

"Sai dai ba za mu yarda da wannan hadarin ba [na tsaurara tsaron kan iyakoki]."

A gefe guda kuma dan wasan tsakiya Scott McTominay da dan baya Axel Tuanzebe, wadanda dukkansu ke fama da rauni, za su je Sifaniya.

United ba za ta koma Ingila ba sai a daren ranar Juma'a kafin wasan Premier tsakaninta da Chelsea a filin wasa na Stamford Bridge ranar Litinin 17 ga watan Fabarairu.