Har yanzu Eden Hazard na yin jinya

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta buga wasan Copa del Rey ranar Alhamis, kuma Eden Hazard ba zai buga wasan ba a Santiago Bernabeu.
Real Sociedad ce za ta ziyarci Real Madrid a wasan daf da na kusa da na karshe.
Hazard dan kwallon Belgium ya yi rauni ne ranar 26 ga watan Nuwamba a wasan Champions League da Paris St Germain.
Dan wasan ya ji rauni ne a karo da ya yi da takwaransa na Belgium, Thomas Meunier a wasan da suka tashi 2-2.
Kawo yanzu tsohon dan wasan Chelsea, bai buga wa Real Madrid wasa 14 ba.
Rashin Hazard bai nuna Real Madrid ba, inda ta ci gaba da cin wasanninta har da lashe Spanish Super Cup da ta yi a bana, bayan nasara a kan Atletico Madrid.
Zinedine Zidane ba zai gangancin saka shi a wasa da Sociedad ba, ganin Real za ta hadu da Manchester City nan gaba a Champions League.
Real din za ta fafata da Sociedad ba tare da wasu fitatten 'yan wasanta da suka hada da Casemiro da Marco Asensio da Lucas Vazquez da Mariano da kuma Dani Carvajal.
Real Madrid ita ce ke kan gaba a teburin La Liga, ya yin da Barcelona ke biye da ita.











