Real Madrid ta karbo Eden Hazard daga Chelsea kan sama da £150m

Bayanan bidiyo, Kalli kwallaye biyar mafi shahara da Eden Hazard ya ci a Chelsea

Real Madrid ta amince ta saye dan wasan Belgium Eden Hazard daga Chelsea kan kudi sama da fam miliyan £150.

Hazard ya amince da yarjejeniyar shekara biyar, kuma za a gabatar da shi a matsayin dan wasan Real Madrid a ranar 13 ga Yuni bayan an diba lafiyar shi.

Dan wasan na Belgium ya zira kwallaye 110 a wasanni 352 a Chelsea tun komawarsa Stamford Bridge daga Lille a 2012.

Hazard ne ya ci kwallaye biyu a wasan da Chelsea ta lashe kofin Europa a makon da ya gabata bayan doke Arsenal.

Dan wasan ya ce barin Chelsea shi ne mataki mafi kalubale da ya taba dauka a rayuwarsa.

Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Eden Hazard ya lashe kofin Premier biyu a Chelsea.

Hazard ya rubuta a shafin shi na Facebook cewa: Ina fatan kun fahimci dole na cika burin sabon babin rayuwata, kamar yadda dukkaninku idan kuka samu dama za su nemi cika burinku.

"Na ji dadin lokacin da na kwashe a Chelsea, kuma babu ranar da na taba tunanin bari don zuwa wani kulub."

Real Madrid za ta fara biyan fam miliyan £89 kan dan wasan, sauran kudaden da za ta biya kari, za su kai ga Chelsea ta kara samun fam miliyan £60 kan cinikin dan wasan.

Baya ga kwallaye 110 da Hazard ya ci, ya kuma taimaka an ci kwallaye 91, daga cikinsu kuma Kwallaye 85 ya taimaka aka ci a Premier.

In addition to his 110 goals, he also made 91 assists for Chelsea. Eighty-five of those goals and 54 of the assists came in the Premier League -

Frank Lampard ne kawai wanda ya ci kwallaye 147 da taimakawa a ci sau 90 da kuma Didier Drogba da ya ci kwallaye 104 da taimakawa a ci 55 suka sha gaban Hazard

Hazard na cikin 'yan wasan mafi shahara na Chelsea a gasar Premier.

Hazard ne dan wasa na uku da Real Madrid ta saya bayan dan wasan gaba Luka Jovic daga Eintracht Frankfurt da kuma dan wasan baya Eder Militao daga Porto.