Eden Hazard ba bawa ba ne - Sarri

Eden Hazard a lokacin da yake wasa a Lille

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Eden Hazard ya koma Chelsea daga Lille a shekara ta 2012

Kociyan Chelsea Maurizio sarri ta tintsire da dariya saboda tambayar da wani dan jarida ya yi masa a lokacin wani taron manema labarai ranar juma'a, dangane da cewa tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon ya ce Chelsea ta ajiye Eden Hazard kamar bawa ne a kungiyar, duk da cewa yana son ya tafi.

Kociyan na Blues cikin dariya ya ce: ''Ban ma san abin da zan ce ba. Bana jin lamarin haka yake.

A cikin watanni uku da suka gabata kullum ina ganin Hazard yana cikin matukar farin ciki. Saboda haka ba na jin gaskiya ne.''

An jima ana maganar cewa dan wasan na Belgium mai shekara 27 yana son tafiya Real Madrid, amma a wannan makon ya ce ba zai tafi kungiyar ta La Liga ba a watan Janairu, na lokacin saye da sayar da 'yan wasa.

Amma dai am ruwaito shi yana cewa shi kam yana jin yana bukatar ya tafi kungiyar domin ya ci lambar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or, abin da kociyan nasa na Chelsea bai yarda da shi ba.

Sarri ya ce, gwanin dan wasa ne, abu ne da ke da kyau da matukar muhimmanci kwarai ya ci gaba da zama a Chelsea.

Ya kara da cewa: ''Ina ganin zai iya cin komai, har ma da Ballon d'Or, a nan ba sai ya je Spaniya ba.

''Misali, idan Chelsea ta iya cin kofin Zakarun Turai kuma Belgium ta ci kofin kasashen Turai, zai iya cin komai ba sai ya yi wasa a Spaniya ba.''