Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na rage albashi don na koma Man United — Ighalo
Odion Ighalo ya ce ya kagu ya koma Manchester United shi ne ya sa ya rage albashinsa don samun damar zuwa Old Trafford da taka-leda.
Dan wasan na tawagar Najeriya ya ce ya yi matukar farinciki da aka amince zai yi wa United wasan aro, kuma ranar bai yi bacci ba.
Mai Shekara 30, daga Shanghai Shenhua ta China zai yi wa United wasannin aro zuwa karshen kakar bana.
Tsohon dan wasan Watford ya ce mahaifiyarsa har kuka ta yi don murna, kuma sai da aka yi biki a kan titin da ya girma.
Ya kara da cewar kungiyoyi da dama sun yi zawarcinsa, amma zuciyarsa ta ce masa ya zabi Manchester United.
Ighalo ya ce da tsakar dare mai kula da harkokin wasansa ya shaida masa cewar United na son daukarsa.
Nan da nan bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi mai fassara harshe suka dunguma zuwa ofishin daraktan Shanghai Shenhua.
Daga nan ne Ighalo da wakilinsa suka kwashe tsawon dare wajen kulla yarjejeniya da cike takardun ka'ida da saka hannu kan a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a Janairu.