Tottenham ta kara ganin barakar Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan wasan da Tottenham ta dauka a Janairun nan Steven Bergwijn ya fara buga mata tamaula da kafar dama, bayan da ya ci Manchester City.
Tottenham ta yi nasarar doke City da ci 2-0 a wasan mako na 25 da suka fafata ranar Lahadi.
Tun farko City ta samu fenatiti, inda Ilkay Gundogan ya buga, amma golan Tottenham, Hugo Lloris ya hana ta shiga raga.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Oleksandr Zinchenko ya yi keta aka kuma ba sshi katin gargadi na biyu, sannan aka yi masa jan kati.
Daga nan ne Tottenham ta samu baraka, inda Son Heung ya fara cin kwallo ta wuce ta kasan hannun mai tsaron ragar City Ederson.
Sai kuma Bergwijn da ya ci na biyu da hakan ya tabbatarwa da Tottenham maki uku rigis.
Hakan ya kai kungiyar mataki na biyar da tazarar maki hudu tsakaninta da Chelsea ta hudu a teburin Premier, bayan buga wasannin mako na 25.
Manchester City tana ta biyu a kan teburi, sai dai kuma Liverpool wadda take ta daya ta ba ta tazarar maki 22,
A makon jiya ne Tottenham ta sanar da daukar Steven Bergwijn daga Kulub din Eredivisie.
Kungiyar ta kuma kara da cewar matashin dan wasa ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a 2025 ta kuma ba shi riga mai lamba 23.
Bergwijn ya fara murza leda a PSV tun yana dan shekara 17, sai dai ya nuna kansa ne a matsayin kwararren dan wasa a tsakanin 2016 zuwa 2017, inda ya yi wa kungiyar ta Netherlands wasa 32.











