Premier League: Man United ta kasa doke Wolves a Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
Sabon cefanen da Manchester United ta yi, Bruno Fernandes kan fan miliyan 47, bai iya tabuka komai ba yayin da Wolves ta rike wa United din wuya a filin wasa na Old Trafford.
A wasan da ba a samu damarmaki ba sosai, Fernandes ya kai 'yan hare-hare, inda ya tilasta wa mai tsaron raga Rui Patricio tare kwallayen, wanda har ma ya kusa saka wata a cikin ragarsa bayan wani shot da Fernandes din ya buga.
Har sai a mintin karshe ne United ta samu kwallo mafi hadari, yayin da Diogo Dalot ya saka wa kwallon da Wan-Bissaka ya bugo kai zuwa gefen raga.
Tawagar ta Ole Gunnar Solskjaer maki hudu kacal ta samu daga wasa biyar da ta buga na baya-bayan nan.
Wolves ta yi bakin kokarinta amma duk da sako nata sabon cefanen na Daniel Podence ba ta iya amfana da kowacce dama ba a gaban raga.
Man United tana saman Wolves a mataki na shida da kuma na bakwai, kowaccensu da maki 35.
Idan Tottenham ta ci wasanta a gobe Lahadi tsakaninta da Manchester City, za ta haye samansu duka da maki 37.







