Bayern Munich ta dauki Alvaro Odriozola

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich ta dauki aron Alvaro Odriozola daga Real Madrid kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.

Mai shekara 24, mai tsaron baya daga gefe, zai koma buga gasar Jamus, bayan da ya yi wa Real wasa biyar a bana.

Odriozola ya koma Santiago Bernabeu daga Real Sociadad a shekarar 2018.

Dan wasan ya buga wa Real Madrid wasa 22 a kakar bara, daga baya aka dai na sa shi a wasa sosai.

Odriozola yana cikin 'yan wasan da suka wakilci Spaniya a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha, amma bai buga wasa ba.

Sai dai ya buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasa hudu ya kuma ci kwallo daya.

Ita ma Ajax ta sanar cewar Bayern ta dauki aron Nicolas Kuhn domin ya yi mata wasa zuwa 30 ga watan Yuli.