Madrid na da dab da daukar Reinier Jesus

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta fara fafutikar daukar dan wasan gaban kungiyar Flamengo kuma dan wasan tawagar matasan kasar Brazil mai suna Reinier Jesus.
Sai dai akwai sauran manyan kungiyoyin Turai irin su Manchester City da Liverpool da PSG da ke neman sa, kamar yadda jaridar AS ta kasar Sifaniya ta ruwaito.
Baya ga yunkurin doke sauran kungiyoyin da Madrid ke son yi wurin daukar dan wasan mai shekara 17, tana kuma son ta dauke shi kafin farashinsa ya yi tashin gwauron zabi.
Farashin dan wasan, in ji AS, ya tashi daga yuro miliyan 30 zuwa 35 a watan Yuli kuma zai ninka nan da shekarar 2021, sannan zai kai har yuro miliyan 70 yayin daukarsa.
Yanzu haka tawagar likitocin Real Madrid tana kasar Brazil domin saka ido kan lafiyar dan wasan.
Wani gidan rediyo a Sifaniya Onda Cero ya ce dan wasan ya kammala wasu daga cikin gwajin likitocin a ranar Juma'a.







