An yaga barakar AC Milan a karshen mako

Asalin hoton, Getty Images
A karshen mako ne Atlanta ta doke AC Milan da ci 5-0 a gasar cin kofin Serie A wasan mako na 17.
Kungiyar karkashin Stefano Pioli tana ta 11 a kasan teburi da makinta 21, kuma karo na takwas aka doke ta a Serie A ta bana.
Da wannan nasarar, Atlanta wadda ke cikin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Zakarun Turai, ta koma ta biyar a saman teburi.
Rabon da a zura wa AC Milan kwallo 5-0, tun bayan wanda Roma ta yi a watan mayun 1998.
Pioli wanda shi ne koci na uku a kungiyar a 2019, ya ce wannan ba Milan ba ce.






