Barcelona: Ansu Fati ya kafa tarihi a Champions League

Matashin dan wasan Barcelona Ansu Fati ya zama mafi karancin shekaru da ya ci kwallo a tarihin gasar Zakarun Turai ta Champions League, bayan ya zira wa Inter Milan kwallon da ta hana ta fito wa daga zagayen rukuni.

Fati mai shekara 17 da kwana 41 ya shiga wasan da Barcelona ta doke Inter Milan ne a minti na 85 da fara wasan kuma mintina kadan da shigowar tasa ya ci kwallo.

Kafin wasan dai da ma Barcelona ta fito zagayen 'yan 16, kuma kafin kwallon ta Ansu Fati sai da Perez ya ci kwallo ba wasansa na farko a Champions League.

Romelu Lukaku ya farke wa Inter Milan a minti na 25 daga wurin yadi na 18, amma kwallon da Fati ya kara ce ta jefa Inter gasar Europa.

"Na bayar da kwallon na ruga sai Luis ya dawo mani da ita. Lokacin da na ci sai filin wasan duka ya yi tsit, ina cike da farin ciki," inji Fati, wanda ya wakilci Sifaniya a tawagar 'yan kasa da shekara 21.

Kocin Barcelona Ernest Valverde ya yaba da kokarin dan kwallon da irin yadda yake da hazaka.

"An haife shi a matsayin mai cin kwallo. Yana dan fama da rauni a yanzu, muna so ya dan huta kadan," a cewar Valverde.

Fati ya ci wa Barcelona kwallo biyu a La Liga a bana, kuma ya buga wasa biyu a Champions League, wanda duk ya shiga a canji kafin wannan da ya buga a San Siro.

A shekarunsa 17 da kwana 40, ya maye gurbin mai rike da tarihin a baya wato Peter Ofori-Quaye, wanda ya ci wa Olympiakos kwallo a wasanta da Rosenborg a ranar 1 ga watan Oktoban 1997, yana da shekara 17 da kwana 195.