Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kocin Faransa ya tsawaita kwantaraginsa zuwa 2022
Kocin Faransa Didier Deschamps ya kara tsawaita kwantaraginsa a matsayin mai horas da 'yan wasa zuwa karshen gasar cin kofin duniya ta 2022 da za ta gudana a Qatar.
Deschamps ya zama kocin kasar ne a 2012 kuma ya kai kasar wasan karshe na kasashen nahiyar Turai na 2016 kafin daga bisani ya samu nasarar daukar kofin duniya na 2018.
Wannan na nufin kocin mai shekaru 51 zai zama mai horaswa da yafi kowanne dadewa rike da kasar. Ya zarce Michel Hidalgo da ya kwashe shekara takwas da wata shida yana jagorancin kunigyar.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Faransa Noel Le Graet ya bayyana matakin kara wa'adin kwantaragin a matsayin "yanke hukunci mai cike da dabara".
A baya dai Le Graet ya ce za a tsawaita kwantaragin Deschamps ne kawai idan har faransa ta samu gurbi a gasar Yuro 2020.
A watan Nuwamba ne Faransa ta samu nasarar fitowa gasar, kuma ta fada rukuni daya tare da Jamus da ta lashe gasar a 2014, da kuma Portugal wadda take rike da kofin.
Sai dai har yanzu ba'a san wanda zai cike daya gurbin ba har sai an buga wasannan share fage nan gaba.
Deschamps wanda a baya kyaftin din Faransa ne ya lashe kofin duniya a 1998, kuma a baya an tsara kwantaraginsa za ta kare ne a karshen gasar Euro 2020.