Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba tabbas ko za mu iya kai bantenmu a bana – Guardiola
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce "babu tabbas" ko Man City za ta iya gwagwaramayar lashe kofuna da manyan kungiyoyin Turai kuma ya kamata "ta gane hakan".
Man City ta sha kashi a hannun babbar abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 2-1 a wasan Premier ranar Asabar, sannan Liverpool ta ba ta tazarar maki 14.
A kakar da ta gabata City ta lashe kofi uku ciki har da kambunta na Premier da ta kare, sai dai tuni ta yi rashin nasara a wasa hudu a kakar bana.
"Wajibi ne mu kara zage damtse sannan mu fahimci abubuwan kuma mu ci gaba da fafatawa," Guardiola ya fada.
Ya ci gaba da cewa: "[Manchester] United na da kwarewar kare gidanta da kuma kwarewar kai hari, dole mu yarda da haka.
"Irin wannan matsalar muke fuskanta daga Liverpool da Barcelona da Real Madrid da Juventus da Manchester United. Wadannan ne kungiyoyin da za mu tunkara kuma ba lallai ne mu iya ba.
"Ya kamata mu fahimci haka a matsayin mu na kulob, mu kara kokari sannan mu ci gaba da fafatawa."
Manchester City ta kare kambunta a karon farko a kakar 2017-2018, inda ta kafa tarihin samun maki 100, amma Liverpool ta doke ta a zagayen kwata fayinal na gasar Champions League.
Ta je irin wannan matsayin a kakar da ta gabata kafin daga bisani Tottenham ta fitar da ita.
Amma duk da haka ta zama kungiya ta farko a Ingila da ta lashe kofunan Premier League da FA Cup da Carabao Cup a shekara guda.