Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Vandevoordt ne gola mafi karancin shekaru a Champions League
Mai tsaron ragar Genk Maarten Vandevoordt ya zama gola mafi karancin shekaru da zai buga gasar Chamipons League yana da shekara 17 da kwana 287, a wasan da za su buga da Napoli.
Wanda a baya ke rike da tarihin shi ne golan Benfica Mile Svilar, wanda ya fara wasansa a gasar Champions da Manchester United a 2017 yana da shekara 18 da kwana 52.
Vandevoordt ya fara buga wa Genk wasanni biyu a gasar kasar Belgium da kuma wani kofi.
Maarten zai fara buga wasan ne bayan an ajiye wanda ke tsaron ragar Gaetan Coucke.
Coucke mai shekara 21 ya buga wa Genk wasa 21 a kakar ta bana, ciki harda duka wasa biyar din Champions. Shi kuma dan kasar Australiya Danny Vukovic bai buga wasa ko wasa daya ba tun 26 ga watan Yuni saboda matsalar dunduniya da yake fama da ita.
An dai hafi dan kasar Belgium din ne a ranar 26 ga watan Fabirairun 2002, ya kuma fara buga babban wasa da Genk a 24 ga watan Satumba.
An kuma fito da shi wasannin uku na gasar Belgium a wannan shekarar.
Masu tsaron raga mafi karancin shekaru da suka buga Champions League
1. Mile Svilar (Benfica) v Manchester United, 18 Oktoba 2017 - Shekara 18 da kwana 52.
2. Iker Casillas (Real Madrid) v Olympiakos, 15 Satumba 1999 - Shekara 18 da kwana 118.
3. Nikolay Mihaylov (Levski Sofia) v Werder Bremen, 31 Oktoba 2006 - Shekara 18 da kwana 125.
4. Igor Akinfeev (CSKA Moscow) v Porto, 14 Satumba 2004 - Shekara 18 da kwana 159.
5. Adrian Semper (Dinamo Zagreb) v Lyon, 14 Satumba 2016 - Shekara 18 da kwana 24.