Ya gaza a Premier ya zama tauraro a Jamus

Serge Gnabry

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Serge Gnabry daya daga cikin 'yan wasan gaba masu hadari a nahiyar Turai

"Arewacin London magoya bayan Arsenal ne" kamar yadda Serge Gnabry bayan kwallo hudu da ya ci rigis a filin wasa na Tottenham a watan Oktoba a gasar Champion.

Ba Spurs ake nufi ba, manyan abokan hamayyar su ake nufi Arsenal, wanda Gnabry ya je yana da shekara 16. Amma yanzu yana Bayern Munich, inda a Jamus din ya zama daya daga cikin 'yan wasan gaba masu hadari a fadin Turai.

Kokarin dan wasan mai shakear 24 a yanzu, ya tuna wa masoya kwallon kafa a Ingila lokacin da yake matashi, inda yake ta kokarin samun gurbi a Arsenal amma daga karshe aka mika shi West Brom aro.

Shekara uku bayan ya bar Ingila, ya fuskanci Tottenham a Munich inda kokarinsa ya taimaka wa kungiyar tsallakawa zagayen siri 'yar kwale, a gasar zakarun Turai, "dan wasa na musamman" inji tsohon mai kocinsa.

Arsenal ta gamsu da fasahar Gnabry kuma ta amince ta biya Stuttgart Fam 100,000 domin daon wasan ya koma makarantar horar da 'yan wasanta idan ya cika shekara 16.

Cikin dan takaitaccen lokaci bayan sanya a kan yarjejeniyar, dan wasan ya zam mutum na biyu mafi karancin shekaru a gasar Premier League a kungiyar Arsenal.

Gnabry ya buga wa Arsenal wasanni 18 a cikin gasa daban-gaban a kakar wasanni biyun farko a matsayin kwararren dan wasa.

Daga bisani ya samu koma baya inda kungiyar ta ba da aron shi ga West Brom a gasar Premier ta shekarar 2015 zuwa 2016.