Inter Milan: 'Ba Conte aka hara da wasikar ba'

Kungiyar Inter Milan ta bayyana cewa ta samu wani sakon wasika cikin ambulan dauke da harsashin bindiga a ciki, sai dai ta musanta cewa kocinta Antonio Conte aka hara.

Jaridar kasar Italiya Corriere della Sera ta ruwaito cewa an aike wa tsohon kocin Chelsea din wasika zuwa gidansa amma Inter ta musanta faruwar hakan.

Ana haka ne kuma matar Conte ta rubuta a shafin sada zumunta cewa: "Ku shaida maganar wasikar nan kanzon-kurege ce!"

Kungiyar Inter Milan ta ce: "Dangane da labarin da aka wallafa a yau (Asabar), Inter Milan tana bayani cewa ba a kai wa Conte wata wasikar barazana ba sannan kuma bai kai rahoton korafi ba.

"Kulob din ne aka aike wa da wasikar kuma kamar yadda aka saba a irin wannan yanayi ya kai rahoto wurin jami'an tsaro."

Antonio Conte dai ya koma Inter Milan ne a farkon kakar bana, inda ya gaji Luciano Spallett.

Yanzu haka Inter Milan tana matsayi na biyu a saman teburin Serie A, yayin da tsohon kulob din Conte Juventus yake saman teburin.