Women Football: 'Yan wasa na yajin aiki a Spain kan albashi

Lokacin karatu: Minti 2

'Yan kwallo mata a kasar Spain suna yajin aiki game da albashin da ake biyansu.

'Yan wasa kusan 200 ne suka saka hannu domin fara yajin aikin a watan Oktoba bayan an shafe sama da shekara guda ana tattaunawa ba tare da cimma matsaya ba.

'Yan matan dai sun bukaci da a samar da dokokin da za su ba su damar samun karin mafi karancin albashi da kyawun yanayin aiki da kuma hutun haihuwa.

Wasannin da aka shirya gudanarwa ranar Asabar sai dage su aka yi sannan kuma guda shida da za a yi a yau Lahadi ma akwai yiwuwar za a dakatar da su.

'Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala tana take-leda ne a Barcelona, abin da ke nufin ita ma tana yajin aikin.

Kungiyar kula da kwallon kafa ta Spain Association of Spanish Footballers ta wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta dauke da shahararrun 'yan wasa kamar golar Athletic Bilbao mai suna Ainhoa Tirapu da kuma Silvia Meseguer ta Atletico Madrid.

A cikin bidiyon sun ce suna fafutika ne saboda 'yan wasan da suka daina take-leda da masu yi a yanzu da kuma "wadanda za su bi sahunmu a nan gaba".

Kungiyoyinsu sun yi tayin biyan yuro 16,000 (sama da naira miliyan 6) a matsayin mafi karancin albashi, amma kungiyoyin da ke wakiltar 'yan wasan sun bukaci akalla yuro 20,000.

Kashi 93% na 'yan wasan da suke buga wa kulob 16 wasa ne suka goyi bayan yajin aikin a wata ganawa da aka yi birnin Madrid ranar 22 ga watan Oktoba.

Kungiyar UDG Tenerife ba ta samu damar zuwa Espanyol ba ranar juma'a saboda dakatar da jirginsu da aka yi bisa matsalar inji, amma sun daura aniyar tafiya ranar Asabar kwatsam kuma sai 'yan wasan suka shiga yajin aiki.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na intanet, kulob din ya ce suna "girmama hukuncin da 'yan wasan suka yanke na shiga yajin aikin".

Ya kara da cewa yana fatan za a cimma yarjejeniya "saboda cigaban kwallon mata da kuma al'umma mai zuwa".