Har sai yaushe Madrid za ta sallami Zidane?

Zinedine Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, PSG sun jawo wa Zidane karin matsin lamba a daren Laraba

Bakin Zinedine Zidane har kunne a wata shida da suka wuce yana cewa ya ji "dadi sosai" da ya dawo gida a matsayin kocin Real Madrid a karo na biyu.

Sai dai murnar ta koma ciki biyo bayan yadda Madrid din ta fara taka-leda a kakar bana, abin da ya kara jawo wa dan kasar Faransar matsin lamba a Bernbeau.

Bayan Real Valladolid da Villarreal sun rike su canjaras a Bernabeu, sai ga PSG ma ta casa su da ci 0-3 a Champions League a daren Laraba.

Mece ce makomar shahararren kocin - wanda ya jagoranci Madrid zuwa ga nasarorin lashe kofin Champions League har uku - kuma wane ne zai maye gurbinsa idan ya bar Real Madrid?

Ko Madrid ta fara gajen hakuri?

Zinedine Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Madrid za ta buga wasa da Sevilla da Atletico Madrid da kuma Osasuna duk a cikin kasa da mako biyu

"Da zarar ka ji irin wannan sakamakon dole ne ka fara duba yanayin da kulab yake ciki," kwararren dan jarida mai sharhin wasannin LaLiga Guillem Balague ya shaida wa BBC.

"Ku saurari abin da 'yan jaridar da ke kusa da Florentino Perez (shugaban Real Madrid) suke cewa, idan suka fara sukar Zidane to ku tabbatar kofa ta bude kenan."

Makin cin wasa na Zidane a Madrid yana kasa da kashi 50% tun bayan dawowarsa a karo na biyu.

Kazalika, wasa bakwai kacal ta ci cikin 16 a LaLiga da Champions League a karkashin Zidane - ta ci biyar, ta yi canjaras hudu.

Sai dai Julien Laurens, shi ma mai sharhi kan wasannin, bai yarda Zidane zai bar Madrid ba, inda ya ce ya san matsalolin kulab din da ma yadda zai gyara al'amura.

"Ya san cewa a karshe abubuwa za su warware," in ji Laurens.

"Ba mutumin da zai karaya ba ne. Ya san matsalolin da ya kamata ya gyara. Wannan tsakiyar ta Madrid ba ta yi kama da ta babbar kungiya ba. Wajibi ne ya gano bakin zaren."

Ko Zidane zai kai Disamba?

Real Madrid ba ta yin wata-wata duk sanda ta amince cewa tana bukatar canji a dakin shiryawar 'yan wasanta.

Ta yi jira har zuwa karshen watan Oktoban bara kafin ta sallami Julen Lopetegui a kakar da ta gabata - wata hudu da rabi ya yi.

Shi kuwa Santiago Solari, wanda ya gaji Lopetegui, an kore shi ne kasa da wata biyar bayan fara horar da kungiyar - abin da ya share fagen dawowar Zidane.

"Idan ya yi sa'a kamar yadda ya faro aikinsa babu mamaki ya kai karshen kakar bana," Ballague ya fada.

"Sai dai salon kwallon kungiyar a yanzu ba shi da kyau. Ko da kuwa Ramos da Marcello da Modric sun dawo ba lallai ne su ishe shi ba ya kai har Disamba."

A gefe guda kuma, dan jarida Kristof Terreur na kasar Belgium sukar kociyan ya yi.

"Me ya kara wa kungiyar? Mene ne salon wasansa? Har yanzu babu tabbacin yadda aka yi Real ta lashe Champions League," a cewar Terreur.

Mourinho zai karbi aikin?

Florentino Perez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Perez da Mourinho na marhaba da juna lokacin da suka hadu a taron Fifa a watan Yuni

An yi ta alakanta Mourinho da aikin horar da Real idan har aka kori Zidane.

A shekarar 2013 ne Mourinho ya bar kulab din bayan zaman shekara uku. Yanzu haka ba shi da aiki bayan Man United ta sallame shi a Disambar 2018.

"Ina zaton Jose Mourinho zai karbi aikin nan da Disamba," a cewar Terreur.

"Real Madrid na bukatar mutum kamar Mourinho wanda ke iya buga wasan tsare baya sannan kuma 'yan wasan ma suna bukatar horo daga tsayayyen koci kamarsa."

Ballague ya ce: "Ai kowa ya san Mourinho na jira."