Champions League: Real Madrid ta sha kashi a hannun PSG

Angel Di Maria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Di Maria ne ya zura kwallo biyu a ragar Madrid

Real Madrid ba ta ji da dadi ba a wasan farko na gasar Zakarun Turai bayan Angel Di Maria ya dura mata kwallo har biyu a filin wasa na Parc des Princes na birnin Paris din kasar Faransa.

Tsohon dan wasan na Real Madrid ya fara cilla kwallo a ragar Thibaut Courtois a minti na 14 bayan Bernet ya koro masa kwallo cikin yadi na 18.

Sai a minti na 33 Di Maria ya kara ta biyu ta hannun Idrissa Gueye, kafin Thomas Meunier ya kara ta uku a mintin karshe na wasan.

Real Madrid ba ta kai hari kai tsaye ga ragar PSG ba a baki dayan wasan wato short on target, wanda rabon da hakan ta faru a Champions League tun kakar shekarar 2003-2004.

Wannan shi ne wasa na farko da aka cinye Madrid a kakar bana, inda ta yi canjaras 2 ta kuma ci biyu a Laligar Sifaniya.

Wannan na zuwa ne yayin da makomar koci Zinedine Zidane ke fuskantar barazana a Bernabeu.