Ole Gunnar Solskjaer: 'A daina yada kiyayya a shafukan Intanet'

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ya dace kamfanonin sada zumunta su rika dakile yada kalaman nuna kiyayya a Intanet.

Solskjaer ya bayyana hakan ne bayan da aka yi wa dan wasansa Paul Pogba kalaman nuna wariyar launin fata a kafafen sada zumunta a farkon makon nan.

Dan wasan Faransa ya kasance mutum na uku da aka yi wa haka bayan ya barar da bugun fanareti a wasansu da Wolves a cikin mako guda.

"Pogba dan wasa ne mai juriya - hakan ya sa dan wasan ya kasance mai kwazo," in ji kocin.

"Dole mu yi wani abu game da hakan kuma mahukunta za su dauki mataki game da hakan."

Solskjaer yana daya daga cikin fitattun mutane da suka bukaci a dauki kwakkwaran mataki dangane da batun a baya-baya nan.

Kazalika, 'yan wasan United kamar Harry Maguire da kuma Marcus Rashford su ma sun bukaci da a dauki mataki.

Tsohon dan wasan kungiyar Phil Neville, wanda shi ne kocin kungiyar mata ta Ingila, ya bukaci 'yan wasan ne da su kaurace wa kafafen sada zumunta domin dakile dabi'ar ta wariya.