Chelsea ta doke Barcelona a wasan sada zumunci a Japan

Tammy Abraham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abraham ya ci kwallon ne bayan tun farko ya zubar da wata kyakkyawar dama

Kwallon da Tammy Abraham da Ross Barkley suka zura ta bai wa Chelsea damar doke Barcelona 2-1 a wasan sada zumunci a Japan.

Abraham ne ya fara zura kwallon bayan da ya yanke gola kafin Barkley ya zura ta biyu.

Ivan Rakitic ne ya zura kwallo dayan da Barcelona ta samu a wasan.

A wasan ne kuma dan wasan da Barca ta sayo kan fam miliyan 107 Antoine Griezmann ya fara buga wasansa na farko.

Christian Pulisic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Christian Pulisic ya koma Chelsea daga Borussia Dortmund a watan Janairu
Antoine Griezmann

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Griezmann ya buga wasansa na farko a Barcelona