Chelsea ta doke Barcelona a wasan sada zumunci a Japan

Kwallon da Tammy Abraham da Ross Barkley suka zura ta bai wa Chelsea damar doke Barcelona 2-1 a wasan sada zumunci a Japan.

Abraham ne ya fara zura kwallon bayan da ya yanke gola kafin Barkley ya zura ta biyu.

Ivan Rakitic ne ya zura kwallo dayan da Barcelona ta samu a wasan.

A wasan ne kuma dan wasan da Barca ta sayo kan fam miliyan 107 Antoine Griezmann ya fara buga wasansa na farko.