Manchester City ta sayi Rodri kan fam miliyan 63

Atletico Madrid midfielder Rodri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rodri ya koma Atletico a watan Mayun 2018 bayan shafe shekara uku a Villarreal

Manchester City na dab da kammala daukar dan wasan Sifaniya Rodri daga Atletico Madrid bayan da ta biya fam miliyan 62.8m.

Atletico ta ce wakilan dan kwallon da na City sun biya kudin ne ranar Laraba domin ba shi damar katse kwantiraginsa.

Bayan haka ne kuma Rodri, mai shekara 23, ya kaste yarjejeniyarsa da Atletico, wacce a da za ta kare a watan Yunin 2023.

Shi ne dan wasa mafi tsada da City ta taba saya a tarihi inda farashinsa ya haura wanda ta biya lokacin da ta sayi Riyad Mahrez a 2018.

Rodri ya koma Atletico a watan Mayun 2018 bayan shafe shekara uku a Villarreal inda ya buga wasa 34 a gasar La Ligar da aka kammala.

City sun matsa a kan dan wasan saboda koci Pep Guardiola na son ya dauki dan wasan tsakiya domin karfafa tawagarsa a kaka mai zuwa.