'Yan wasa 6 da za su iya barin United a karshen kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ka iya kyale 'yan wasanta har shida su bar kunbgiyar a karshen kakar wasa ta bana a yayin da suke yunkurin karfafa kiungiyar karkashin sabon koci Solskjaer.
Sai dai har yanzu akwai rashin tabbas game da makomar Ander Herrera da Juan Mata da kuma Alexis Sanchez.
Solskjaer zai iya sayar da Sanchez amma girman albashin dan wasan ka iya dakatar da masu zawarcinsa.
Kungiyar dai na kan tattaunawa da Herrera da Mata, wadanda kwamtiraginsu zai kare a karshen kakar wasa ta bana.
Sai dai babu tabbas ko za a cimma wata yarjejeniya da daya daga cikinsu. Wata majiya ta shaida wa BBC cewa tuni Herrera ya amince ya koma kungiyar PSG a kaka mai zuwa, amma babu tabbaci daga wakilansa ko kuma kungiyar ta PSG.

Asalin hoton, Getty Images
Shi kuwa Sanchez wasanni biyar kawai ya fara a kakar bana ya kuma shigo a matsayin canji sau shida sai kuma kwallo daya da ya ci tun bayan da Solskjaer ya maye gurbin Mourinho a United.
Duk da haka akwai kungiyoyi da za su iya biyan albashin nasa sai dai ba a san wacce ce ba, musamman ganin yadda tauraruwarsa ta rage haskakawa tun bayan barinsa Arsenal a Janairun 2018.

Asalin hoton, Getty Images
A wasu bayanai da Der Spiegel ta wallafa a watan Mayun shekarar 2018 sun bayyana cewa kwantiragin Sanchez zai kai har 2022, inda yake karbar fam dubu £391,000 duk mako, da kuma karin £75,000 a kowanne wasa da aka fara da shi.
Haka kuma dan wasan mai shekara 30 yana karbar fam miliyan 1.1 duk shekara tare da wasu alawus-alawus.
Fitar da 'yan wasa shida za su yi daga kulob din na United ita ce mafi girma tun a shekarar 2015, lokacin da Louis van Gaal ya saki 'yan wasa shida, wadanda suka hada da Di Maria da Tom Cleverley da Anders Lindegaard.
Dan wasan da United take hankoron ta rike shi ne David de Gea, kuma ta yi imanin zai ci gaba da zama.

Asalin hoton, Getty Images
An toshe damar da De Gea yake da ita a cikin kwantiraginsa ta barin United a watan Nuwamba, wanda hakan zai sa ya ci gaba da zama har zuwa 2020.
Duk da cewa babu yarjejeniya har yanzu tsakanin kungiyar da mai tsaron ragar, United na da kwarin gwiwar cimma matsaya don samun kyakkyawar yarjejeniyar.











