Najeriya za ta yi wasan sada zumunci da Ingila

Najeriya da Ingila za su fafata a wasan sada zumunci a shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha.

Ingila ce za ta karbi bakuncin Najeriya a filin wasa na Wembley a yau Asabar da misalin karfe 5:15 agogon Najeriya.

Karawar kamar zakaran gwajin dafi ne ga kasashen biyu kafin fara gasar cin kofin duniya.

Ingila da Najeriya sun taba haduwa sau biyu, inda suka tashi wasa babu ci a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2002.

Ingila kuma ta taba doke Najeriya ci 1-0 a karawar da suka yi a 1994.

Najeriya za ta sake karawa da Jamhuriyar Czech a wasan sada zumunci a ranar Laraba kafin tawagar ta Super Eagles su nufi Rasha.

Najeriya za ta fara fafatawa ne tsakaninta da Croatia a gasar cin kofin duniya a ranar 16 ga watan Yuni, kafin ta fafata da Iceland da kuma Argentina a rukuninsu na D.

Ingila kuma za ta sake buga wasan sada zumunci da Costa Rica a ranar Alhamis kafin tawagar kasar su nufi Rasha.

Ingila na rukunin G, inda za ta fara karawa tsakaninta da Tunisia.