Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Atletico Madrid sun iso Najeriya
Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta Spaniya ta isa Najeiya domin karawa da tawagar kwallon kasar ta Super Eagles.
A ranar Litinin ne da daddare 'yan wasan na Atletico, wadanda su ne zakarun Turai na Europa League, suka isa birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Za a yi wasan na sada zumunci ne ranar Talata da misalin karfe 6:00 agogon Najeriya a wani bangare na shirye-shiryen da kasar ke yi domin tunkurar gasar cin kofin duniya.
'Yan wasan da Athletico ta taho da su sun hada da:
Oblak, Werner, Juanfran, Sergi, Montero, Solano, Jota, Rafa Muñoz, Thomas, Gabi, Vitolo, Toni Moya, Agüero, Olabe, Mikel Carro, Joaquín, Torres, Correa, Gameiro da kuma Borja.
Akwai dai manyan 'yan kwallonsu irinsu Diego Costa da Griezmann da ba a taho da su ba domin wasan, wanda za a yi ranar Talata a filin wasa na Godswill Akpabio.
Najeriya na yin atisaye a birnin na Uyo, inda a nan ne ta yi wasannin share fagen shigarta cin kofin duniya, domin tunkarar Rasha 2018 da za a fara a watan gobe.
Super Eagles tana rukuni guda da Argentina, da Croatia da kuma Iceland a gasar ta cin kofin duniya.