Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Russia 2018: Super Eagles ta fitar da sunayen 'yan wasa 30
Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr ya fitar da kwarya-kwaryar sunayen 'yan wasa 30 wadanda daga cikinsu ake saran za su wakilci kasar a Gasar Cin Kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni a kasar Rasha.
Cikin 'yan wasan akwai tsohon dan wasan Chelsea Mikel Obi da Ahmed Musa da Odion Ighalo da Victor Moses da dai sauransu.
A cikin wadannan 'yan wasan ne kocin Super Eagles din zai zabi 'yan wasa 23 wadanda za a tafi kasar Rasha da su don fafatawa a gasar wadda za a fara ranar 14 ga watan Yunin bana.
A ranar 4 ga watan Yuni ne kocin zai aikewa hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) sunaye 'yan wasa 23.
Najeriya tana rukunin D ne wanda ya kunshi kasashen Croatia da Iceland da kuma Argentina.
A shirye-shiryen tunkarar gasar, tawagar kasar za ta yi wasannin sada zumunci da DR Congo a ranar 25 ga watan Mayu, sai karawa da Ingila a ranar 2 ga watan Yuni.