Hanyoyi 5 da Arsene Wenger ya sauya kwallon kafa

Arsene Wenger ya daga kofunan da ya lashe

Asalin hoton, JOHN STILLWELL

Bayanan hoto, Wenger ya lashe kofin kalubale na FA da na League a shekararsa ta biyu a kungiyar Arsenal

Yayin da kocin Arsenal Arsene Wenger ya sanar da cewa zai yi murabus bayan shafe shekara 22 a kulob din, an yi nazari a kan irin sauye-sauyen da ya kawo a kulob din, da gasar Premier da kuma kwallon kafa kanta.

Gagarumin sauyi a duniya

Gasar Premier wadda Wenger ya shiga a 1996 bayan maye gurbin Bruce Rioch, wanda shi ma ya taka rawar gani, ta sha bambam da wacce zai bari a watan Mayu.

Duk da cewa Wenger Bafaranshe ne, mafi yawancin 'yan wasan kulob din turawa ne, kuma ya taka muhimmiyar rawa a cikinsu.

Ba a jima da nada Wenger a matsayin kocin Arsenal ba, 'yan wasa suka samu damar shiga ko ina a kasashen turai ba tare da matsi ba.

Wannan layi ne

Nan da nan kuma ya kware wajen gano 'yan wasa masu bajinta musamman daga Faransa da kuma kasashen Afirka da ke amfani da harshen faransanci, sannan ba a jima ba ya ya hada hadaddiyar kungiyar da ta kunshi zakakuran 'yan wasan kwallon kafa.

Shekaru tara bayan kasancewarsa kocin Arsenal, sun lallasa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace da ci 5-1 a shekarar 2005, daga nan ne ya sauya 'yan wasansa, inda ba bu wani bature ma a ciki.

Irin abincin da 'yan kwallonsa ke ci

Arsene Wenger a Monaco

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arsene Wenger a Monaco

Kulob din da Wenger ya ke kafin ya dawo Arsenal, shi ne Nagoya Grampus 8 da ke Japan, inda Wenger ya gano cewa babu masu kiba a ciki.

Ya ce "Dukkan wata rayuwa ta dogara ne da samun cikakkiyar lafiya. Abincin da ake ci a tsohon kulob din da na bari baya wuce kayan lambun da aka dafa da kifi da kuma shinkafa, a ingila ana cin abinci bil hakki da gaskiya, kuma ana shan siga da nama sosai ba tare da an hada da kayan lambu ba".

Ya fara wannan tsarin cin abinci da ya bari a baya a sabon kulob dinsa wato Arsenal.

Al'adar shan barasa ta yi kaurin suna a harkar kwallon kafar Ingila, lamarin da ya haddasa matsalolin da suka shahara a kafafen watsa labarai ga Adamas da Merson. Haka kuma cin abinci mai nauyi kafin wasanni batu ne da ya kankane hirarrakin da 'yan jarida ke yi da 'yan wasa.

A wasa na farko da Wenger ya jagoranta aka daina ba da cakulet Mars, abin da ya sa 'yan wasan suka yi dan karamin bore.

Sai dai daga karshe Wenger ne ya yi nasara. Aka daina ba da nau'ikan abinci irin su taliya, aka koma ba da ganyayyaki.

A shekarun 1990 ba a jin batun abinci mai gina jikin 'yan wasa - amma yanzu ba zai yiwu ba a ce ba a samu kwararru ba suna tsara ko wanne sinadari da ke cikin irin abincin da 'yan wasa ke ci a gasar Premier.

Ya daukaka wasan kwallon kafa zuwa wani mataki

Arsene Wenger a filin wasa na Emirates

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Arsene Wenger a filin wasa na Emirates

Ba a taba samun kocin da ke da kyakkyawar mu'amala da 'yan wasansa kamar Wenger ba.

Kungiyar ta yi tashe a karshen 1980 da farkon 1990, inda suka rika amfani da 'yan wasansu kamar Niall Quinn ko Alan Smith suna zura kwallo a ragar abokan hamayya, sannan kuma sun rika tsaron bayansu da kyau.

Amma shi kungiyar da ya hada daban ta ke da ta baya, saboda suna da 'yan wasa kamar Thierry Henry da kuma Dennis Bergkamp.

A lokacin da suke tashe, kwallon da suka buga ta rinka burge jama'a saboda yadda suke rike kwallo da mikata ga abokan wasansu.

Sabbin nasarori

Arsene Wenger da Patrick Viera

Asalin hoton, PA/ROTA PA ROTA

Bayanan hoto, Wenger da Viera

Labarin kofinsa na farko da ya samu, shi ne lokacin da ya rika kokarin ganin sun buge kungiyar Manchestre United, abin ya birge jama'a sosai kuma ba za a taba mantawa da lokacin da kulob dinsa ya zurawa Manchester kwallo 1-0 a filin wasansu na Old Trafford ba.

Haka kuma a shekarun 2003 zuwa 2004, Wenger ya yi tashe sosai.

Kungiya daya ce - Preston North End ta taba shafe kakar wasa ba tare da ta fadi a wasa ko daya ba.

An dauka abu ne da ba ya yiwuwa a kakar wasa mai wasanni 38.

Amma kuniyar Arsenal karkashin Arsene Wenge ta taka irin wannan rawar. A lokacin yana da masu tsaron baya kamar su Ashley Cole, Kolo Toure da Sol Campbell, kuma Patrick Vieria ne ke jagorantar 'yan wasan kungiyar.

Wannan layi ne

Arsenal ta buwayi dukkan kungiyoyin da ta kara da su har wasanta na karshe da kungiyar Leicester inda ta lashe wasan da ci 2 da 1.

Babu kungiyar da ta iya kamo wannan kokarin har yanzu.

A kashin gaskiya ma, sun cigaba da cin wasanninsu har sai da suka kai wasanni 49, wanda ya kawo karshe a yayin da ta kara da Manchester United - wanda ya ja hankulan masoya wasan kwallo har aka lakaba ma wannan karawar "pizzagate" a Oktobar 2004, domin wani dan wasa ya jefi Sir Alex Ferguson da fanken pizza.

Fitattun 'yan wasan da suka bar Wenger a Arsenal

  • Jens Lehmann: Ya bar Arsenal a 2008 ya koma Stuttgart lokacin da kwantiraginsa ta kare a kungiyar daga baya ya yi ritaya. Ya sake koma wa tamaula a 2011 daga nan ya sake shiga Arsenal.
  • Bacary Sagna: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Landa.
  • Kolo Toure: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.
  • Thomas Vermaelen: A shekarar 2014 ya koma Barcelona.
  • Ashley Cole: Ya koma murza-leda a Stamford Bridge ita kuwa Chelsea ta bayar da William Gallas.
  • Patrick Vieira: Ya koma wasa ne a Juventus.
  • Cesc Fabregas: A shekarar 2003 ya koma murza-leda a Barcelona.
  • Marc Overmars: A shekarar 1997 ya koma Barcelona domin maye gurbin Luis Figo.
  • Alexis Sanchez: Ya komaOld Trafford, inda Manchester United ta bayar da Henrikh Mkhitaryan.
  • Robin van Persie: A shekarar 2012 ya koma murza-leda a Manchester United.
  • Thierry Henry: Ya koma buga tamaula a Barcelona a 2000.

Kalaman da aka san Wenger da su

Arsene Wenger ya nuna damuwarsa saboda korar da aka yi wa golan Arsenal Jens Lehmann a gasar kofin zakarun Turai ta 2006

Asalin hoton, ODD ANDERSEN

Bayanan hoto, Arsene Wenger ya nuna damuwarsa saboda korar da aka yi wa golan Arsenal Jens Lehmann a gasar kofin zakarun Turai ta 2006

Yawancin manajoji na da wasu kalamai da ake alakantasu da su - a misali Bill Shankly ya taba cewa "Wasu mutane sun dauki lamarin kwallon kafa a matsayin na a yi rai ko a mutu... amma lamarin ya fi haka muhimmanci." - Shi ma Wenger na da kalaman da za su kasance tare da shi har karshen rayuwarsa: "Ban ga lokacin da abin ya faru ba."

Abin ya fara ne a lokacin Wenger na sabon kocin Arsenal - inda ya ke amfani da kalmomin domin ya kaucewa rashin kamun kan 'yan wasansa da aka nuna masu jan kati sau 52 a kakar wasa guda 7.

Ya kan rika cewa bai ga lokacin da aka aikata laifi ba, saboda haka ba zai iya cewa komai ba.

Ya rika fakewa da wadannan kalaman domin ya guji sukan 'yan wasansa a bainar jama'a - amma ya kasance wani abin zunde a gareshi saboda yawan fadin kalaman da ya rika yi.

Amma da alama dabarar ta yi masa amfani. Wasu ma na ganin cewa a fagen rayuwa, ba a fagen kwallon kafa ba ma, manyan mutane kan kaucewa fadawa cikin matsaloli idan suka ce ba su ga abin da faru ba, duk da cewa a gaban idonsu aka aikata abin.

Wa ya san manyan mutane nawa ne suka tsira da mutuncinsu sabili da wadannan kalaman na Wenger?

Arsenen Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arsene Wenger a wajen wani taron