Arsenal za ta auna kwazon Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce shugabannin kungiyar za su auna kokarinsa a matsayin koci a karshen kakar bana.
A farkon kakar bana Wenger ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu domin ci gaba da jan ragamar kungiyar, zai kuma yi kaka 21 a Gunners kenan.
Wenger ya ce zai so jin abinda shugabannin Arsenal za su ce kan aikin da yake gudanarwa a Emirates.
Arsenal ta kammala a mataki na biyar a gasar Premier da ta wuce, kuma karon farko kenan da kungiyar ta kasa shiga gasar cin kofin Zakarun Turai tun bayan shekara 20 a jere tana zuwa.
Arsenal tana matsayi na biyar a kan teburin Premier bana da maki 16 bayan wasa tara da ta buga a gasar.







