Arsene Wenger zai bar Arsenal a bana

Asalin hoton, Reuters
Kocin kulob din Arsenal Arsene Wenger zai bar kungiyar a karshen kakar bana, bayan da ya shafe kusan shekara 22 a kulob din.
Kocin dan kasar Faransa, zai bar kungiyar ne shekara daya kafin sabuwar kwantiraginsa ta zo karshe.
Kulob din dai shi ne na shida a teburin Premier kuma akwai yiwuwar ba za su samu damar zuwa gasar Zakarun turai ta badi ba
Wenger, mai shekara 68, ya ci wa kungiyar Kofin gasar Premier sau uku da kofin FA bakwai, da suka hada da wadanda ya dauka a lokaci daya a shekarun 1998 da 2002.
"Na ji dadin samun damar jan ragamar kulob din na tsawon wasu shekaru da ba zan manta ba," a cewar Wenger.
"Na ja ragamar kungiyar da dukkan azama da mutunci.
"Ina kira ga duk masoyan Arsenal, ku kula da mutuncin kungiyar."
Za mu kawo muku karin bayani nan ba da jimawa ba.
Kulob din na Arsenal ya ce nan ba da jimawa ba za a nada wani sabon koci.

Asalin hoton, Arsenal
Babban mai hannun jari a kulob din Stan Kroenke ya bayyana sanarwar a matsayin mataki mafi tsauri da ya taba dauka a duka shekarunsa a harkar wasanni.
Ya kara da cewa "Daya daga manyan dalilalan da suka sa muka shiga harkar Arsenal shi ne saboda abinda Arsene ya kawowa kungiyar da kuma daga darajarta"
"Ba za a taba kwatanta irin yadda yake kaunar kulub din ba da kuma irin jajircewarsa a harkar wasanni." In ji Stan Kroenke.
An nada Wenger kocin Arsenal ranar daya ga Oktoban 1996, a yanzu shi ne koci mafi dadewa a gasar Premier, sannan ya jagoranci wasanni 823.











