Ba zan so Wenger ya zauna a Arsenal ba - Ian Wright

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright ya ce ba zai iya bayar da goyon baya Arsene Wenger ya ci gaba da zama a matsayin kociyan kungiyar ba bayan kakar nan.
Wright ya ce ko kociyan ya ci gaba da zama a karshen kakar nan, shi kam ba zai goyi da bayan hakan ba, kuma ya san cewa da wuya a ce wani zai nemi ya ci gaba da zama.
Ya ce dole ne a kawo karshen wannan abin da ake yi a kungiyar na bambadanci da ganin ido.
Tsohon dan wasan ya kuma zargi wasu 'yan wasan da samun kudin banza a kungiyar ba tare da cin guminsu ba yana mai cewa mai kungiyar Stan Kroenke bai damu da hakan ba.
Arsenal ta sha kashi a wasanninta shida daga cikin 12 a shekarar nan ta 2018, na baya bayan nan shi ne wanda Manchester City ta doke ta a wasan karshe na cin kofin Carabao ranar Lahadi.
Wright ya ce har kullum Wenger ba ya rasa ta cewa, sannan kuma yana shagwaba 'yan wasa







