Barcelona tana taka rawa a kakar bana

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barcelona ta ci dukkan wasanninta na La Liga da na kofin Zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na taka rawar gani a kakar wasan kwallon kafa ta bana ta 2017/18.

Barcelona ta ci wasa bakwai da ta yi a La Ligar da ake yi, ta kuma ci wasa biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champion League, jumulla ta ci karawa tara kenan.

Hakan ya sa kungiyar tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 21, ita ce kuma ke kan gaba a rukuni na biyu a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

A wasa taran da ta yi ta ci kwallo 27 an kuma ci ta guda biyu kacal.

Tun fara kakar bana a Turai, PSG ta ci karawa tara a wasa 10 da ta yi, ta kuma yi canjaras sau daya.