Afghanistan: Yadda Taliban ke tabbatar da bin dokokin rufe fuska da jiki da tsayar da gemu a titunan Kabul

- Marubuci, Daga Secunder Kermani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kabul
Cikin dogayen fararen rigunansu, masu bincike daga ma'aikatar kula da tarbiyya ta Taliban sun fi kama da masu duba abinci sama da masu "lura da tarbiyya".
Amma su ne a gaba-gaba wajen tabbatar da sabon salon, na tabbatar da cewa 'yan Afghanistan suna suffatuwa da tsarin Musulunci.
Rawar da za su taka gagaruma ce.
Yayin wata ziyara da suka kai wani katafaren kantin zamani da ke Kabul watanni biyu baya, masu tsare wajen sun ce an rika duba lokacin lalacewar kayayyaki, sun kuma riƙa umartarsu su rika cire hoton mata da ke nuna jikinsu a jikin kayan sayarwa.
Daga baya an mayar da hotunan da yawa, kamar inda suka gani lokacin da suka koma ziyarar gani da ido a wannan makon, tare da wakilin BBC.
Duk da cewa shi ne ƙarami a cikin tawagar, ɗan makarantar mai shekara 25 Maulvi Mahmoud Faith shi ya jagoranci tafiyar.
Da yake bayani ga masu tsare shagunan, ya nuna masu mahimmancin addua'a da kuma ajiye gemu.
Ya yi magana ne a matsayin ɗan uwa da kuma ba da shawara. "barin gemu misali ne irin na biyayya ga Annabi Muhammad," a cewarsa, kuma "yana da wani alfanun na daban".
"Wannan malamin yana da mata biyu ko uku," yana nuna daya daga cikin masu ziyarar da suka zo tare, "wata hanya ce ta samun iko."
Wasu labaran masu alaƙa

Shi da sauran abokan aikinsa hudu, sun nuna sha'awarsu ta taimaka wa masu aikin wajen share hawayen matsalolin da suke fama da su.
Lokacin da wani mai aikin kantin ya yi korafin cewa, wani mutum yana matsa masa cewa sai ya ba shi sabuwar waya kuma shi dan Taliban ne, Maulvi sai ya rubuta ƙorafin tare da lambar mutumin ya ce za su yi bincike.
Amma sabuwar dokar da ma'ikatar da ta shafi mata ta sanya gyale mai rufe fuskokinsu ita ce ta fi jan hankali - da kuma suka.
A farkon wannan watan ne, aka yi dokar cewa dole mata su riƙa rufe fuskokinsu a cikin mutane. Duk matar da aka samu rahoton tana yin hakan a kai-kai za a aike mai lura da shi gidan yari.
Maulvi bai yi wannan batun ba a cikin makalar da ya gabatar a kantin, kuma lokacin da aka tambaye shi kan lamarin, sai yace "yanzu maganar maza muke yi ba ta mata ba."
Game da sabon tsarin sanya tufafi sai ya ce, "mun bai wa masu shagon shawara su sanya hoton yadda ya kamata a yi."
Ana wa Afghanistan kallon kasa mai ra'ayin riƙau, wadda tuni mata ke sanya nikabi domin rufe fuskokinsu.
A birane kamar Kabul wasu na sanya dan kwalin da zai rufe musu gashin kansu ne kawai, a baya-bayan nan kuma wasu na hadawa da takunkumin fuska saboda annobar korona.
Masu rajin kare hakkin mata a ciki da wajen kasar sun rika mayar da martani cikin bacin rai kan sabuwar dokar, da ta hana duk kananan yara zuwa sakandire da hana daukarsu aiki.
Shekaru da yawa 'yancin mata na fuskantar koma baya a kasar.
A wasu lokutan, ba a damu da dokar sanya hijabi ba sosai.
Amma da yawa na fargabar Taliban za ta iya matsawa kan lamarin - saboda dokar da aka sanya wa mata masu gabatar da shiri a gidan talabijin na sanya gyalen da zai rufe fuskokinsu.
A cikin birni, har yanzu ana iya ganin matan da ba sa rufe fuskokinsu, an kuma gabatar da wasu da dama lokacin da wakilan ma'aikatar suka je ziyarar.
"Mu na ware matan da suke sanya Hijabi da wadanda ba sa sanyawa," in ji Maulvi Fatih a hira da BBC.
"Idan mace ta wuce gona da iri, ta yi shigar da bata dace ba, da sanya tufafin da bai dace ko ba su rufe fuska, lallai za mu nemo muharraminta."
Ya ce kawo yanzu, ba a kai ga hakan ba, ko da yake da wuya a iya gano abin da ya ke nufi kai tsaye da kalmar wuce gona da iri.
Da aka tambayi wani hurumi ma'aikatar ke da shi na irin tufafin da matan Afghanistan za su sanya, sai Maulvi Fatih sai ya kada baki ya ce: "Ba hurumin ma'aikata ba ne, ba kuma wani ya sanya dokar ba, wannan dokar Allah ce…
"Abin da ke janyo matsaloli da aikata zunubi shi ne fuska, idan fuskar mace a bude ta ke ba to menene amfanin hijabi?"
Yawancin Musulmai a sassa daban-daban na duniya, ba amince dole sai mace ta rufe fuskarta ba.

Masu sanya ido, kan cika bayan mota a Hilux, su na zagayawa zuwa tashar motocin bas.
Su na fito da duk wanda bai bi doka ba daga mota, su na duba ko maza na zama a kusa da mazan da ba muharramansu ba, da duba ko ana bai wa mata kujerar zama ko ana bari su tsaya a cikin motar.
Ma'aikatar ta yi kaurin suna wajen aikata muggan ayyuka, idan akai waiwaye lokacin da Taliban ke jan ragamar kasar a shekarun 1990, inda akan lakadawa masu laifi duka.
Maulvi Fatih ya shaida mana cewa za a hukunta wadanda suka aikata laifin fiye da sau daya, da direbobin motar da suka bari maza da matan da ba muharraman juna ba suka zauna wuri guda.
Sannan idan direbobin suka taka doka, ya na bada umarnin ''a kai mutum ofishinsu na kwana guda."
A nan a kan yi musu nasiha da jan hankali domin su bi dokokin da Allah ya shimfida, zai kwana ana yi ma sa nasiha, da gari ya waye sai a sallame shi."
A kan idonmu, wasu jami'ai cikin tsanaki da nutsuwa suka tafiyar da jama'ar da aka kawo masu laifi.
Daga baya mazauna yankuna daban-daban sun yi magana da mu inda sukai korafi kan cin zarafi da dukan da jami'ai ke yi musu.
Amma ga alama kama-karyar Taliban na ƙaryuwa.
Waya mai rajin kare hakkin mata Leila Baseem tana cikin wata motar bas da jami'an Taliban ɗin suka tare suna bincike kan matan da ba su rufe fuskarsu ba.
Wani mai bincike ya doki bayan motar don tsayar da ita sannan ya shiga ciki.

Ms Baseem ta shaida wa BBC cewa "mata biyu na sanye da burka," sauran kuma irina suna sanye da baƙaƙen riguna da takunkumin rufe fuska... Sai na ce masa, babu wacce ba ta sanya hijabi ba a nan."
Ms Bassam ta ce "da jin haka sai ya tafi cikin fushi."
"Bai kalle ni ba amma sai ya ce, 'ku mata ne marasa kunya. Wannan ba Afghanistan ɗin da kuka sani ba ce, Jamhuriyyar Musulunci ce a yanzu. Ba za mu sake yin abin da kuke so ba."
Ms Baseem wadda ta taɓa jagorantar wata ƙwarya-ƙwaryar zanga-zangar adawa da matakin Taliban na rufe makarantun sakandaren mata, ta ce jami'in ya zarge ta da cewa tana yi wa "Amurka aiki ne" kuma a yanzu tana son yi rayuwa irin ta Amurkawa, kafin daga bisani direban motar ya roƙe ta da ta yi shiru kar ta sake tankawa jami'in.
Wasu direbobin sun shaida wa BBC cewa an gargaɗe su kar su ɗauki matan da ke sanye da suturar da ta ɗame musu jiki, duk da dai sun ce, a yanzu jami'in hukumar ɗabbaka tarbiyya ta Vice and Virtue, ba su hana mata yin tafiya ba don ba su rufe fuskarsu ba.
A watan Agustan bara da Taliban ta karɓi mulki, sun nuna kamar za su sassauta kan aƙidun da mutane ke tsoron su ɗabbaka musu, suka kaucewa sabbin dokokin yadda al'umma za su yi rayuwarsu.















