Yakin Ukraine: Wace ce Nato kuma ta yaya taje taimaka wa Ukraine?

Nato soldiers in Serbia, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Ministoci daga ƙasashe mambobin Nato na tattaunawa kan yadda za su ci gaba da taimakon Ukraine wajen kare kanta daga kutssen Rasha.

Ministan harkokin wajen Ukraine ya yi ta tambayarsu batun "makamai, makamai, makamai".

An ruwaito cewa Jamhuriyar Czech, wata ƙawar Nato, ta aika tankokin yaƙi zuwa Ukraine.

Amurka na samar wa da Ukraine wani sabon jirgi marar matuƙi wanda ke iya kai wa tankokin yaƙi hari.

Mece ce Nato?

Nato - the North Atlantic Treaty Organization - kungiyar kawancen soji ce da kasashen 12 da suka hada da Amurka, da Canada, da Birtaniya da Faransa suka kafa a shekarar 1949.

Burinta shi ne ta yaki fadadar bayan yaki na kasar Russia a kasashen Turai.

Kasar Russia ta Soviet ta mayar da martani ta hanyar kaf ana ta kwancen sojin na gabashin kasashen Turai masu tsarin kwaminisanci da ake kira Warsaw Pact.

Bayan rgujewar Tarayyar Soviet Union a shekarar 1991, kasashe da dama na tsohuwar kungiyar kasashe kawancen soji ta Warsaw Pact suka sauya sheka zuwa kungiyar tsaro ta Nato.

Yanzu kawancen na da kasashe mambobi 30.

Mambobin sun amince sun taimaka wa juna a duk wani lokaci na kai farmaki kan ko wace kasa mamba.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Me yasa Nato ba ta aike da dakaru zuwa kasar Ukraine ba?

Saboda Ukraine ba mamba ba ce a cikin kungiyar kawancen ta Nato, ba a bai wa kungiyar damar taimaka wa kasar ba.

Kana kasashen kawancen Nato na fargabara cewa muddin dakarunsu suka yi fito-na-fito da dakarun kasar Russia a Ukraine, zai haifar da daukacin tashin hankali tsakanin Russia da kasashen Yamma.

Nato ta ce kasashe mambobinta a shirye suke su taimaka wa Ukraine,'' amma dole ta tabbatar da cewa yakin bai fadada zuwa wajen kan iyakar kasar ta Ukraine ba.

Haka ne ya sa Nato ta yi watsi da kafa yankunan da ba za a iya kai farmaki ta sama ba a kan kasar Ukraine.

Amma kuma, ta amince da aikewa da sabbin bataliyoyi hudu zuwa kasashen Slovakia, da Hungary, da Bulgaria da kuma Romania - wanda uku daga ciki sun yi iyaka da kasar Ukraine - da ya sa kasancewar Nato ya linka sau biyu a yankin.

Wannan layi ne

Me yasa Ukraine ba ta zama mamba a Nato ba?

Nato ta yi wa Ukraine tayin hanyoyin shiga kungiyar a shekarar 2008. Bayan da kasar Russia ta karbe yankin Crimea a shekarar 2014, Ukraine ta bai wa shiga kungiyar muhimmanci.

Amma hakan bai faru ba, saboda adawar da kasar Russia ta dade tana nunawa a kai.

Daya daga cikin bukatun kasar Russia kafin kutsawarta shi ne cewa kada a taba bari Ukraine ta shiga cikin - abinda kawancen ya ki amincewa ya goyi baya.

Russia na fargabar cewa Nato na kokarin yin kutse wa yankunanta ta hanyar daukar sabbin mambobi daga gabashin Turai, kana cewa shigar da Ukraine zai sa dakarunta su shiga kusa da yankinta.

Shugaban kasar Ukraine Zelensky ya amince cewa kasarsa ba za ta iya shiga cikin kungiyar ta Nato a halin yanzu ba, yana mai cewa: ''a fili ta ke cewa Ukraine ba mamba ba ce a kungiyar tsaron ta Nato. Mun fahimci wannan."

Wannan layi ne

Wadanne irin makamai ne Birtaniya da sauran kasashe suka aike zuwa Ukraine?

Gabanin zaman tattaunawar Nato a birnin Brussels, Birtaniya ta bayyana cewa za ta samar da sabbin makaman kariyar nukiliya da fan miliyan 25 don taimaka wa Ukraine biyan alawus na sojojinta.

Tuni Birtaniya ta samar da karin makaman kakkabo tankunan makamai masu linzami na NLAW fiye da 4,000. Ta kuma aike da wasu na'ukan makamai masu linzami na Starstreak

Ukrainian soldier with a Javelin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan Ukraine na riƙe da wata ƙatuwar bindiga a wania tisaye a 2021

Har ila yau ta bayar da rigunan sulke da hulunan kwano da takalman boot.

Kana, Birtaniyar ta aike da na'urorin kariya ta sama masu cin dogon zango na Sky Sabre zuwa kasar Poland, tare da sojoji 100 da za su tafiyar da su.

Da farko Amurka ta aike da dala miliyan 200 kwatankwacin fan miliyan 152 na makamai, Sun kuma hada da makamai masu linzami na Javelin masu siffar mashi, da Stinger masu kakkabo jiragen sama da rigunan sulke.

Tuni Amurka ta sanar da bayar da tallafin dala biliyan daya na samar da tsaro. Sun kuma hada da karin makaman zamani masu cin dogon zango irin su.

Jamhuriyar Czech ta ce za ta samar da makaman da kudinsu ya kai dala miliyan 45 kwatankwacin fan miliyan 34, da suka hada da tankokin yaki.

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta ce za ta kashe euro miliyan 450 kwatankwacin fan miliyan 376 don tallafa wa Ukraine wajen sayen makamai.

Turkish fighter jets on patrol for Nato over Poland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nato na ƙara ƙaimi wajen kare tsaro a gabashin Turai

Shi ne karon farko a cikin tarihi da kungiyar ta EU ke tallafawa wajen samar da makamai a wani fagen yaki.

Ita ma kasar Jamus, ta janye dadadden tsauraran matakanta kan samar da makamai wa fagen yaki. Za ta aike da makamai da dama zuwa Ukraine.

Kasashen Netherlands, da Belgium, da Poland, da Estonia, da Latvia da kuma Slovakia na cikin kasashen da za su aike da kayan yaki da suka hada da albarusai da makamamashi fa kayan abinci.

Wannan layi ne

Dakaru nawa Nato ke da su a gabashin Turai?

Tun kafin a amince da aikewa da dakaru na baya-bayan nan, Nato tana da dakaru tun daga yankunan Baltic a arewacin kasar Romania daga kudanci.

An girke su a can tun a shekarar 2014, bayan karbe yankin Crimea da Russia ta yi, kana an tsara su yadda za su zama cikin shirin ko-ta-kwana ko da kasar Russia za ta kai hari.

Nato ta aike da wasu daga cikin zarataanta 40,000- zuwa Gabashin Kasashen Turai da ke da kan iyakoki da Russia da Ukraine.

Tana da jiragen yaki da ke cikin shirin ko-ta-kwana da kuma jiragen ruwa 120, da suka hada da bataliyoyin soji uku da ke sintiri daga arewa mai nisa zuwa gabashin tekun Bahar Rum.

Amurka ta yi alkawarin aikewa da karin dakaru zuwa Turai - wadanda suka hadu da sauran bataliyoyi hudu na kasashe daban-daban, Nato na da kasashen Estonia, da Latvia, da Lithuania da kuma Poland, da kuma rundunarta da kasashen a kasar Romania.

Wannan layi ne