Hanyoyin gyaran jiki ga matan da suka wuce shekara 50

BBC

Ga duk macen da ta wuce shekara 50, da kuma ta san cewa kyau na farawa ne daga cikin jiki, amma kuma wacce take son kyawunta ya fito, akwai shawarwari da dama da masana a fadin duniya ke bayarwa.

Fitowa cikin karfin gwiwa, da yarda da kai - wadannan duka muhimman hanyoyi ne na jin cewa ka yi kyau.

Amma kuma kamar ko wace mace da ba ta taba tsayawa a gaban mudubi ba za ta iya fada maka, sirrin yadda mutum yake yin kyau shi ma yana da matukar muhimmanci.

A yayin da yanayin yadda kamanninmu kan kasance daya daga cikin abubuwan da ke nuna ko mu su wane ne, ganin cewa ka yi kyau wani abu ne na kara karfafa gwiwa.

Ba sai mace ta kashe kudi da yawa ko kuma ta sha wahala za ta gyara jikinta ya yi kyau ba.

Masana sun bayyana cewa akasarinmu ba sa bukatar mayar da hankali kan manyan abubuwan gyaran jiki - akwai wasu muhimmai da kan taimaka wajen sanyawa mu yi kyau ba tare da aljihu ya yi kuka sosai ba.

Wata mujallar kiwon lafiyar dan adama a Amurka WebMD, ta tattauna da ƙwararru a fannin kula da lafiyar fatar jiki da kuma gyaran jikin.

Sun bayyana ra'ayinsu daban-daban game da abubuwan da suka kamata matan da shekarunsu suka wuce 50 za su yi don kula da kansu wajen yin kyau da nagarta.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Tasirin yawan shekaru kan fatar jiki da kuma gashin kai

Yadda fata ke tauyewa ko tamoji, da kuma furfurar gashi, sauye- sauyen da ke zuwa da yawan shekaru ne, da kuma abu ne wanda ba za a iya kauce wa ba.

Amma kuma masana sun ce mace za ta iya amfani da kayayyakin gyaran fata, da kuma gyaran fuskar da bai danganci sai an yi tiyata ba, da kuma kayayyakin gyaran gashi da inganta shi.

Akwai hanyoyi da dama ga matan da suka wuce shekaru 50 za su bi wajen inganta kamanni da kuma kyawunsu.

Dadewa a cikin rana, da shan taba, da yanayin abinci, da kuma gado, duka suna nunawa a jininki a lokacin da kike kara shekaru, kamar yadda wasu kwararru suka bayyana a mujallar ta WebMD.

Har ila yau in ji mujallar, suƙewa, da naunaya, da kuma ƙiba ko teɓa na shafar yanayin fatar jiki.

Don haka a yayin da mace ke kara shekaru, fatar jikinta ba ta iya sake sabbin kwayoyin halitta cikin sauri kamar yadda ta saba yi.

Don haka, sannu a hankali ta zan zama babu sulbi kuma za ta rika yawan bushewa.

Wani abu mai kama da hakan kuma kan shafi kwayoyin halittar da ke sa gashi yin launi. Amfanin sinadarin kwayoyin halittar gashi kan yi karanci a lokacin sabunta launin shi, wanda ke sa gashin ya yi furfura.

Wannan layi ne

Salon matan Najeriya na gyaran jiki saboda shekaru

Wasu matan da suka haura shekaru 50 a Najeriya, sun bayyana wa BBC yadda suke yi wajen ganin sun inganta kyawun fata da sauran sassan jikinsu don su rika yin kyau a kullum.

Malama Aisha Umar Sani ta bayyana cewa da farkon fari ta kan hada wasu abubuwa da ba a rasa ko wace mace da su a cikin dakin girkinta wajen gyaran fatar jikinta.

"Na kan yi amfani da garin kurkum da aka fi sani da 'tumeric' a Turance, sai in hada da madara in kwaba in rika shafa wa ya dade a jikina kafin in shiga wanka," in ji Aisha.

A wasu lokutan na kan rika dama kurkum din da madara ina sha, don na ji masana na cewa shi ma yana sa fatar jiki kyau da kuma karko, kuma ina ganin sauyi sosai," ta ce.

Akwai hanyyoyi da dama da mata ke bi don inganta fatar jikinsu har ma da gashi don kaucewa tsufa da wuri, kamar yadda Aisha ta jaddada.

"Kin ga yanzu an cigaba sosai, akwai maguguna da mayuka da akan shigo da su daga kasashen waje masu gyara fata da kuma aka tabbatar ba su da wata illa saboda ana sarrafa su ne daga ganyaye da saiwoyi da kuma sauran tsirrai."

Hadiza Mohammed ita ma ta shaida wa BBC cewa akwai hanyoyi masu sauki da mace za ta bi wajen guyar jikinta da za ta yi karko da kuma kyau a ko da yaushe.

''Ina bibiyar masana kiwon lafiya, da gyaran jiki a kafofi daban- daban na sada zumunta, ina karuwa da abubuwan da suka kamata in yi wajen gyara jikina, kuma ina ganin amfanin abin,'' in ji Hadiza.

Amma kuma ta ce gaskiya mata da dama saboda tsadar rayuwa ba sa iya samun sukunin sayen irin magungunan da Malama Aisha ta bayyana aka shigo da su daga wajen, da ke maye gurbin sinadaren da fatar jikin ke rasawa idan ta kara shekaru.

"Akwai su da dama kam, ko da yake akwai masu saukin kudi amma duk da haka za ka ga wani lokaci dole ka hakura ba bi wata hanyar," ta ce.

"Na kan samu ganyen itacen dogon yaro ''neem'' in kirba shi in kwaba da kurkum da kuma zuma in rika shafawa a jikina ya dade, sai in yi wanka, amma akwai wahala da cin lokaci."

Wannan layi ne

Wasu labaran masu alaka

Wannan layi ne

Wasu daga cikin hanyoyin gyaran jikin matan da suka haura shekaru 50

Fatar jiki

1. Kada ki sha taba, ko kuma ki daina shan taba idan kina sha

Shan taba in ji masana na daya daga cikin manyan abubuwan da ke sauran lalata fata da kuma nuna alamun tsufa ga masu shan ta musamman mata.

Sun bayyana cewa tana lalata garkuwa da sinadaran da ke inganta fatar jikin cikin sauri ta yadda zai yi matukar wahala ta gyaru. Don haka su kan yi gargadi game da hakan.

2. Guji yawan shiga rana

Masana sun ce ki guji shiga rana musamman daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana. A lokacin ne rana ke zafi sosai.

Idan kuma har fita ta kama ki to ki tabbatar kin sa abin da zai rufe fuskarki kamar malafa da riga mai dogon hannu da tabaran ido.

3. Amfani da mayukan kare zafin rana a kai-akai

Rika amfani da mayukan da ke kunshe da akalla kashi 7 bisa dari na sinadarin zinc oxide da na SPF 30 a kullum -- wadanda ke dauke da kariya daga abubuwan da ke kunse cikin zafin ranar da ke yi wa fatar jiki illa.

Ki sabunta shafawa a fatarki da ke waje musamman ta fuska a ko wane sa'oi biyu a lokacin da kika fiya waje.

Zafin ranar kan haifar da sakamako irin na sauye-sauye ga fata kamar yamutsewa ko dusashewar launin fatar.

4. Yawan zuwa a duba fatar saboda kansar fatar jiki

Idan akwai wasu sauye-sauye da suka dame ki, tutunbi likitan fata ba tare da bata lokaci ba.

Wadanda ke da hasken fata da kuma shekarunsu suka haura 50 sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar kansar fatar, don haka yana da matukar muhimmanci a rika zuwa wurin likita.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

5. Tattalin fatar jikin da ta bushe

Bushewar fatar jiki alamu ne babba da ke nuna cewa akwai babbar matsala ta rashi ko karancin wasu sinadaran da ke sa fatar jikin nagarta.

Don haka yana da matukar muhimmanci ki rika amfani da na'urar saka damshi, kana ki yi amfani na sabulai da mayukan shafawa mai saka laushen fata. Ki kuma rika tuntubar likita idan kina da wata matsala.

6. Cin abinci mai kyau da yawan shan ruwa;

Cin abinci mai gina jiki shi ma yana gyarawa tare da inganta lafiyar fatar jiki. Kana ki rika yawan shan ruwa don yana taimaka wa matuka wajen sa fatar jiki yin laushi daga ciki har waje.

7. Gwada yin amfani da magugun da mayukan hana fata tsufa

Idan shekarunki suka haura 50, mayukan shafawa da wasu magunguna a shuguna kan taimaka wajen inganta lafiyar fatarki.

Za su taimaka wa kwayoyin halittar fatar jikinki su samar da sinadarin collagen da ke inganta kyau da nagartar fatar jiki.

8. Motsa jiki

Baya ga cin abinci mai gina jiki da macen da ta haura shekaru 50 ya kamata ta rika yi, haka shi ma motsa jiki na da matukar muhimmanci.

Motsa jiki na taimaka wa wajen kara samun lafiya da kuzari, da kuma hana tumbi wanda daya daga cikin abubuwa ne da ke sa mace kara tsufa da wuri, baya ga matsalolin da tumbin ke haifar wa lafiyar jiki.

Kana kada ki rika cin abinci mai nauyi da kafin ki kwanta, hakan yana haifar da zaunewar kitse ko kuma tumbin da kan saka mace muni, da rashin karfin guiwar saka kayan kawa na shiga jama'a.

Wannan layi ne

Gashin kai

Gashin kai muhimmn abu ne wajen cikon kyau da kwarjinin mace, musamman wacce shekaru suka haura 50, lokacin da karfinsa, da kyaunsa, da kuma walkiyarsa da tsayinsa kan ragu mayuka.

Don haka akwai bukatar kulawa ta musamman da ya kamata ki yi wa gashin kan ki a daidai wannan lokaci da galibi furfura kan fito a kan gashin.

Babu wata waraka da ake samu daga fitowar furfura a gashi, wannan wani mataki ne na yawan shekaru da ko wane dan adam ba zai iya kaucewa ba.

Masana sun bayyana cewa furfura na faruwa ne sakamakon karancin wani sinadarin kwayoyin halitta da ake kira melanocytes da ke saka launin gashi asali da nagarta da kuma sheki, da zarar babu shi hakan ke sa ya rika yin furfura.

Za ki iya runa shi ya koma baki ko kuma wasu launuka da kike bukata, ta hanyar amfani da sinadaran runin da suka dace.

Sinadarn runa gashin kan boye furfurar ne zuwa dan wani lokaci, wanda sai kina yi kina kara shafa wa a duk lokacin da kika bukaci yin adon gashi, ko kuma kitso don ya kara miki kyau da kuma kwarjini.

Amma kuma masana sun bayyana cewa dole ne a rika taka-tsan-tsan wajen zabar irin yanayin sinadaran runa gashin da ya kamata a yi amfani da shi don kauce wa illolin da wasu kan haifar.

Malama Aisha ta shaida wa BBC cewa ta kan shafa lalle ne ya jima a kan ta idan ta bukaci rufe furfurar.

''Lalle ba shi da ill awa gashin kai, said ai kuma bay a saka shi ya yi ainihin launinsa na baki kamar yadda sinadarn kanti ke yi, yakan yi ja ne,'' in ji ta.

''Kawai dai s hi lalle ba zai ba ka launin bakin ne ba, amma kuma gashin ka yana kara yin nagarta.''

Sauya yanayin yadda mace za ta rika gyaran gashinta wani cikamakon abu ne na karin kyau a koda yaushe.

Mace za ta iya yin kitso ko kuma ta je wurin gyaran gashi a yi mata wani salo da ban wanda zai yi daidai da fuskarta.

Kada ki rike al'adar nan ta yanke gashi da matan da shekarunsu suka yi nisa ke yin a kin barin dogon gashi.

Komai tsayin sa akwai abubuwan da za ki iya yi ba tare da kin gajiya ba wajen kula da gashin kan ki, kamar yadda idan ba shi da tsayi za ki iya gyara shi yadda zai yi miki kyau.

Akwai sabulan ruwa na wanke gashi da mayukan da za ki iya samu a kananan da manyan shaguna da za ki rika amfani da su wurin kulawa da gashin don ya kara yawa da sheki, wanda daya daga cikin abubuwan da za su kara miki kyau ne komai shekarunki.

Ko ma menene zabin ki, kula da kan ki ya zarta komai da za ki yi a rayuwarki.

An tsakuro wasu daga mujallar kiwon lafiyar jikin dan adam WebMD ta Amurka

Wannan layi ne